'Yan Kasuwa na Shirin Sauke Farashin Fetur zuwa N700 bayan Sabani da Dangote
- Wasu manyan ‘yan kasuwa a fannin mai sun cimma yarjejeniya da masu samar da fetur daga waje domin shigo da kaya masu rahusa
- Rahotanni sun nuna cewa sabon tsarin zai iya rage farashin litar man fetur zuwa kimanin N700 a Najeriya
- Shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya ce hauhawar matatar Dangote na tilastawa ‘yan kasuwa neman mafita daga kasashen waje
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa manyan ‘yan kasuwa a bangaren man fetur a Najeriya sun shiga yarjejeniya da wasu kamfanoni na kasashen waje domin shigo da fetur mai rahusa.
Wata majiya da ke da kusanci da yarjejeniyar ta bayyana cewa kudin shigo da litar man zai kai kusan N650, wanda hakan zai sa a rika sayarwa a kasuwa a kan N700.

Source: Getty Images
Leadership ta wallafa cewa sabon tsarin zai taimaka wajen rage wahalhalun tsadar mai a Najeriya idan har ya tabbata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabanin 'yan kasuwar mai da Dangote
Shugaban kungiyar masu gidajen sayar da man fetur (PETROAN), Billy Gillis-Harry, ya bayyana cewa rashin daidaiton farashin mai a matatar Dangote na jefa su cikin matsin tattalin arziki.
Legit ta rahoto cewa shugaban ya ce:
“Bankuna na bin mu bashi saboda muna sayen kaya, kafin mu kai su tashoshi farashin ya sauya, hakan na sa mu asara. Wannan lamarin yana kassara kasuwancinmu.”
Ya ce ‘yan kasuwa na bukatar sahihan bayanai daga kasuwa domin su iya tsara harkokinsu da zuba jari cikin kwanciyar hankali.
Shugaban ya kuma bukaci bude hanyoyi masu sauki na sayen kaya da ajiyar fetur a rumbunan ajiya.
Ana fargabar dawowar dogayen layin mai
Gillis-Harry ya ja kunnen cewa idan ba a dauki mataki ba, akwai yiwuwar sake fuskantar dogayen layuka a gidajen mai saboda ‘yan kasuwa da dama ba za su iya cigaba da sayen fetur ba.
Ya ce:
“Ni ma da kaina ba zan iya saye ba saboda ba ni da kuɗi. Matatar Dangote na canza farashi kai tsaye bayan mun saya da tsada. Wannan ya jefa mu cikin rashin riba.”
Ya kara da cewa hakan na tilasta masu shigo da kaya da dama su nemi hanyoyi daga waje domin samun ragin farashi da dawowa kasuwa don samun riba.

Source: Getty Images
Dangote ya soki shigo da man fetur daga waje
Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya jaddada cewa dogaro da shigo da kaya daga waje barazana ce ga ci gaban Afrika da ‘yancin tattalin arzikin ƙasa.
A cewarsa:
“Muddin muna shigo da abin da muke iya samarwa da kanmu, ba za mu taba cigaba ba. Matatar man nan hujja ce cewa za mu iya gina masana’antu da suka kai matakin duniya.”
Dangote zai kawo sauyi a harkar mai
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya ce nan gaba kadan zai kawo gagarumin sauyi a harkar man fetur.
Dangote ya ce sauyin da zai kawo zai shafi dukkan harkokin mai, ba ma kawai abin da ya shafi sauke farashi ba.
Aliko Dangote ya bayyana haka ne bayan shugaba Bola Tinubu da wasu manyan 'yan kasuwa sun ziyarci matatar shi da ke Legas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


