Abba Kabir Ya Jajantawa Hamza Al Mustapha kan Babban Rashi da Ya Yi
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya jajanta wa Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya bisa babban rashi da ya yi
- Gwamna Abba ya aika da ta'aziyyar kan rasuwar yayarsa Hajiya Rakiya Mustapha Mai Koko, wadda ta rasu bayan rashin lafiya
- Abba Gida Gida ya bayyana cewa marigayiyar uwa ce ga dangi, da ke da hakuri da da juriya, a jawabinsa kuma ya yi mata addu'a
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sakon ta’aziyya ga Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya bisa rashin da ya yi.
Gwamnan ya yi ta'aziyyar kan rasuwar yayarsa, Hajiya Rakiya Mustapha Mai Koko bayan fama da jinya.

Source: Facebook
Sakon ta'aziyyar Abba Kabir ga Hamza Al-Mustapha
A cewar wata sanarwa a Facebook, mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, marigayiyar ta rasu ne kwana biyu da suka gabata.
Gwamna Yusuf ya bayyana Hajiya Rakiya a matsayin uwa ga dangin Mustapha, mai hakuri da juriya.
Ya ce wannan rashi ba na danginta ba ne kadai, har da Musulmai da kasa baki ɗaya, inda ya ce gibin da ta bari ba mai cikewa ba ne.
Abba Kabir ya yi ta'aziyyar rasuwar malami
Haka zalika, Gwamna Abba Kabir ya jajanta wa iyalai da almajiran Sheikh Abdulmumini Badako na Dawakin Tofa bisa rasuwar fitaccen malamin addinin.
Gwamnan ya bayyana Sheikh Badako a matsayin ginshikin ilimi da da tarbiyya, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimi da jagoranci.
Ya ce ayyukan Sheikh za su ci gaba da jagorantar mutane a hanyar ilimi, ibada da tausayi a cikin al'umma baki ɗaya.
Ya yi addu’ar Allah ya jikan mamatan, ya sa su huta a Aljanna Firdausi, ya kuma bai wa iyalansu hakurin jure wannan babban rashi.

Source: Facebook
Iyalan marigayin sun godewa Abba Kabir
Daya daga cikin ƴaƴan marigayin, Mukhtar Abdulmumin ya yi godiya ta musamman ga Gwamna Abba Kabir.
Mukhtar ya yi godiya ne kan ta'aziyyar da Abba Kabir ya yi musu bisa rasuwar mahaifinsu a shafinsa na Facebook.
Ya ce:
"Muna godiya bisa sakon ta’aziyyar da ka aiko dangane da rasuwar mahaifinmu, Sheikh Abdulmumin Yunusa Badako.
"Kalamanka masu taushi da addu’o’inka na neman rahamar Allah sun zama gata da kwantar da hankali a gare mu.
"Allah ya saka da alheri bisa jagoranci da tausayi irin naka, mun gode sosai."
Waye Hamza Al-Mustapha?
Manjo Hamza Al-Mustapha, ɗan asalin jihar Yobe, tsohon jami’in soja ne wanda ya shahara a zamanin mulkin marigayi Janar Sani Abacha.
An haife shi a shekarar 1960, kuma ya shiga rundunar sojin Najeriya inda ya yi fice saboda kwarewa a fannin tsaro da leken asiri.
A lokacin mulkin Abacha daga 1993 zuwa 1998, Al-Mustapha ya rike mukamin Babban Jami’in Tsaron Shugaban Kasa, kuma yana daga cikin mafi kusa da Abacha a fadar gwamnati.
A matsayinsa na CSO, Al-Mustapha ya kafa ƙungiyoyi na musamman da ke kula da tsaron shugaban kasa, ciki har da rundunar "Strike Force" da "Body Guard Unit", wadanda ke da manyan kayan aiki da izini kai tsaye daga sama.
A lokacin mulkinsu, ya kasance mutum mai karfi da tasiri, kuma an danganta shi da wasu lamurra masu rikitarwa da suka faru a lokacin, ciki har da zargin take hakkin dan Adam da kashe-kashen siyasa.
Bayan mutuwar Abacha, Al-Mustapha ya fuskanci shari’u da zaman gidan yari har na tsawon shekaru, kafin daga bisani kotu ta soke tuhumar da ake masa a 2013.
Duk da rikice-rikicen siyasa, Al-Mustapha ya ci gaba da kasancewa cikin manyan ‘yan Najeriya da ke da tasiri a harkokin tsaro da siyasa.
Abba Kabir ya miƙa ta'aziyya ga gwamnan Jigawa
Mun ba ku labarin cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya na daga cikin mutanen da su ka halarci jana'izar mahaifiyar gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi.
An tabbatar da cewa Hajiya Maryam Namadi ta rasu a safiyar Laraba 25 ga watan Disambar 2025 wanda ya sa gwamna Abba ya jagoranci tawaga zuwa Jigawa a yammacin ranar.
Abba Kabir ya roki Allah ya yi mata rahama ya kuma sanya ta a aljannar Firdausi madaukakiya, yayin da ya ke ba iyalanta hakurin wannan babban rashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


