Kaduna: Kwacen Waya Ya Zama Ruwan Dare, Yan Daba Sun Hallaka Soja
- Wasu miyagun matasa sun jawo asarar ran babban jami’in sojin ruwa Commodore M. Buba a lokacin da suke kici-kicin kwace masa waya
- Rahotanni sun tabbatar da cewa M. Buba ya tsaya domin gyara tayar motarsa da ta samu matsala a Kawo ta jihar Kaduna a lokacin da lamarin ya afku
- An ga wasu mahara sun yo kan jami'in suna kokarin kwace masa masa da sauran kayan da take tafe da su, amma rikici ya kaure a tsakaninsu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – An kashe wani babban jami’in sojin ruwa ta Najeriya, Commodore M. Buba a unguwar Kawo da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa a jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan daba ne suka kai masa hari a wajen tashar motoci ta Kawo yayin da yake kokarin tsallaka titin.

Source: Original
Channels TV ta ruwaito cewa ‘yan daban sun yi kokarin kwace wayarsa da sauran kayayyakin da ke hannunsa a kusa da gadar Kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun tabbatar da kisan jami’in tsaro
Solacebase ta ruwaito cewa majiyoyin tsaro sun bayyana cewa jami’in, wanda ke karatun kwas din manyan hafsoshi a makarantar AFCSC Jaji, ya tsaya a kusa da gadar domin ya sauya taya motarsa da ta yi faci.
Yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa Jaji, wani daga cikin ‘yan daban ya tare shi tare da neman wayarsa, shi kuma sai ya hana shi.
Wasu ganau sun ce da jami’in ya ki mika wayar, sai daya daga cikin maharan ya caka masa wuka a kirji, lamarin da ya jawo zubar jini.
Rahotanni sun ce wani dan sintiri dake kai kawo a wajen ya yi ƙoƙarin ceton sojan amma shi ma mutum ya daɓa masa wuƙar a hannunsa.
Masu kwace sun kashe soja a Kaduna

Kara karanta wannan
Ana tsaka da shagalin Sallah, mutane sun tafka asarar biliyoyin Naira a jihar Kano
Rahotannin sun cigaba da cewa an garzaya da jami’in asibiti cikin gaggawa, amma likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu kafin a kawo shi.

Source: Facebook
Yanzu haka, an adana gawar Commodore M. Buba a babban asibitin rundunar sojin kasa ta Najeriya, wato 44 Nigerian Army Reference Hospital.
Bayan aukuwar lamarin, wasu matasa sun taru a wajen, suka kama wanda ake zargi da kai harin, suka yi masa dukan tsiya har lahira.
Yan daba sun kashe matashi a Kano
A baya, mun ruwaito cewa wasu bata-garin matasa sun kashe malamin addini kuma kwararre a fannin fasaha, Alaramma Jabir Lawan Abdullahi a unguwar Gidan Sarki da ke cikin birnin Kano.
Lamarin ya faru a lokacin da ake gudanar da wata kilisa a yankin, inda wasu bata-gari suka farmaki Alaramma Jabir tare da caccaka masa wuka sau da dama kafin su tsere daga wajen.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Haruna Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya ce tuni rundunar ta haramta gudanar da kilisa saboda irin wannan.
Asali: Legit.ng
