'Komai Ya Wuce:' Tinubu Ya Yafewa Gwamnan Legas Laifin da Ya Yi Masa
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa yafe dukkanin abubuwan da Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi masa
- A wata ganawa da kwamitin GAC, Tinubu ya ce daga yanzu, ba ya rike da Sanwo Olu ko wasu daban a ransa a halin yanzu
- Rahotanni sun ce akwai sabani tsakanin shugaban ƙasa da Sanwo-Olu tun bayan tsige kakakin majalisar dokokin jihar Legas
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya daina fushi da Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata ganawa da kwamitin dake baiwa gwamnan jihar Shawara (GAC) da aka gudanar a ranar Lahadi a Legas.

Source: Twitter
Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa Gwamna Sanwo-Olu da wasu yan GAC sun kai wa shugaban ƙasa ziyara a gidansa dake Ikoyi, yayin da ake rade-radin cewa akwai sabani tsakaninsa da shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan
Bangarori 3 da yan adawa da kungiyoyi ke ganin gazawar gwamnatin Tinubu a shekaru 2
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rokawa gwamnan Legas afuwar Tinubu
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa jiga-jigan da suka halarci ganawar sun roƙi gafara a madadin gwamnan, kuma shugaban ƙasa ya yafe.
A ranar Asabar da ta gabata, Tinubu ya kau da kai ga Sanwo-Olu a yayin kaddamar da kashi na farko na aikin hanyar gabar teku ta Legas zuwa Kalaba.
Bikin ya samu halartar manyan ‘yan APC, daga ciki har da tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan, Gwamna Babagana Zulum, Gwamna Douye Diri na Bayelsa, da Gwamna Bassey Otu na Kuros Riba.
Tinubu ya gaisa da manyan baki ta hanyar miƙa musu hannu, amma ya kau da kai daga Gwamna Sanwo-Olu inda ya miƙa hannu kai tsaye ga Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo, wanda ke tsaye kusa da shi.
A ranar Alhamis, Gwamnan Legas bai halarci bikin kaddamar da aikin gyaran titin da ke kaiwa tashar jiragen ruwa mai zurfi a jihar ba, wanda Tinubu ya jagoranta.
Tinubu ya daina fushi da gwamnan Legas
Rahoton ya ci gaba da cewa yayin ganawar da aka yi, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ba ya fushi da kowa, balle Gwamna Sanwo-Olu.

Source: Facebook
Tinubu ya ce:
“Komai ya ƙare. Na yafe komai.”
Bayan wannan furuci, Gwamna Sanwo-Olu da sauran 'yan GAC sun durƙusa gaban shugaban ƙasa don nuna girmamawa da neman yafiya.
Sai dai duk da wannan ganawa, shugaban ƙasa da gwamnan ba su bayyana ainihin abin da ya faru tsakaninsu ba.
Amma ana zargin cewa Tinubu da Sanwo-Olu sun samu sabani tun bayan tsige Mudashiru Obasa daga matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Legas.
Ndume ya ki marawa Tinubu baya
A labarin, kun ji cewa Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa bai goyi bayan matakin gwamnonin jam’iyyar APC 22 da ke son shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake tsayawa takara a 2027 ba.
Ndume ya bayyana cewa a shekarar 2015, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya samu goyon bayan gwamnoni 22 na jam’iyyar PDP, amma hakan bai hana shi faduwa a zabe ba.
Ya kara da cewa a lokacin da aka fara kokarin kada kuri'a a kan goyon bayan Tinubu ya zama dan takarar APC a zaben 2027, ya fice daga Banquet Hall inda ake gudanar da taron a Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
