Hawan Sallah: Gwamna Abba Kabir Ya Buƙaci Diyya daga Gwamnatin Tarayya

Hawan Sallah: Gwamna Abba Kabir Ya Buƙaci Diyya daga Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnatin Kano ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya diyya saboda soke bukukuwan hawan sallah na shekara biyu da suka wuce wanda ya jawo asara
  • Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu, Alhaji Tajo Uthman shi ya bayyana haka a Kano
  • Uthman ya ce soke hawan ya janyo asarar tattalin arziki, yana mai cewa lokaci ya yi da za su bukaci diyya kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta yi korafi kan hana hawan sallah da rundunar yan sanda ta yi a jihar Kano.

Gwamnatin ta bukaci gwamnatin tarayya da ta biya diyya bayan an soke bukukuwan hawan sallah na shekaru biyu a jere.

Gwamnatin Kano ta bukaci diyya daga Tinubu
Gwamnatin Kano ta bukaci diyya kan hana hawan sallah. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Abba Kabir Yusuf.
Source: Twitter

Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu, Alhaji Tajo Uthman, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, yayin gaisuwar Sallah, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da shagalin Sallah, mutane sun tafka asarar biliyoyin Naira a jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminu Ado Bayero ya soke hawan sallah

Wannan sanarwa ta biyo bayan matakin yan sanda na hana hawan sallah saboda matsalolin tsaro a jihar.

Fitar da sanarwar ke da wuya, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya janye shirin hawan sallah da aka saba yi kowace shekara.

An dauki matakin ne bayan shawarar da aka yi da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin Kano.

Mai martaban ya ce zaman lafiya da tsaron jama’a ya fi komai muhimmanci a wannan lokaci da ake fuskantar kalubalen tsaro.

Sanusi II ya hakura da hawan sallah

Shi ma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya soke hawan sallah da ya fara shirin yi a jihar saboda masalahar jama'a.

Sanusi II ya bayyana haka ne a daren ranar Alhamis, 5 ga watan Yuni, 2025 bayan tattaunawa da wakilan gwamnatin jihar Kano.

Sanusi II ya janye hawan sallah a Kano
Aminu Ado Bayero ya janye hawan sallah a Kano. Hoto: Sanusi II Dynasty, Masarautar Kano.
Source: Facebook

Asarar da Kano ta yi kan hana hawa

Kara karanta wannan

Yadda dakarun sojin Najeriya suka yi bikin sallah a fagen daga a Borno

Kwamishinan kananan hukumomi a Kano, Tajo Uthman ya ce jihar ta yi asarar makudan kudi saboda dakatar da wannan biki na al’ada da ke jawo hankalin baki.

Sanarwar ta ce:

“Hukumar UNESCO ta amince da hawan sallah a matsayin bikin al’ada.
"A lokacin bikin, Kano na samun kudaden shiga daga baki da ‘yan cikin gida."

Ya ce soke bukukuwan ya yi tasiri sosai a kan kasafin kudin jihar da kuma ci gaban tattalin arziki na Kano, cewar Daily Post.

Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya dole ne ta dauki alhakin illar tattalin arzikin da soke bikin ya jawo kuma ta biya diyya.

Ya ce:

“Lokaci ya yi da za mu bukaci diyyar asarar da aka yi."

Uthman ya kuma bukaci a dawo da gudanar da bukukuwan Durbar nan take, yana mai cewa sokewar da aka yi abin takaici ne.

Yan sanda sun hana hawan sallah a Kano

A baya, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Kano ta sake soke shirin bukukuwan hawan sallah yayin da ake shirin sallar layya.

Ƴan sanda sun jaddada haramcin hawan sallah a Kano saboda barazanar tsaro kamar yadda ta faru a lokacin bikin ƙaramar sallah.

Wannan mataki dai ya ci karo da sanarwar da masarautar Kano ta fitar, wacce ta gayyaci hakimai zuwa zuwa hawan babbar sallar bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.