Hajji Ya Kare: An Saka Ranar Fara Dawo da Alhazan Najeriya daga Saudiyya

Hajji Ya Kare: An Saka Ranar Fara Dawo da Alhazan Najeriya daga Saudiyya

  • Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa za a fara dawo da ‘yan Najeriya daga Saudiyya daga ranar 13 ga Yuni 2025
  • Za a fara dawo da mahajjata daga jihohin Imo, Bauchi, Kebbi da Sokoto ta jiragen Air Peace, Max Air da Flynas
  • Shugaban NAHCON ya gode wa ma’aikata, hukumomin jin daɗin alhazai da gwamnatin tarayya bisa goyon bayan da suka bayar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da cewa za a fara dawo da mahajjatan Najeriya daga ƙasar Saudiyya daga ranar 13 ga watan Yuni, bayan kammala ibadar Hajjin 2025.

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Usman, ne ya bayyana hakan a Mina ranar Juma’a, a lokacin da musulmai a duniya ke gudanar da bukukuwan sallar layya.

Kara karanta wannan

Tsohon mawakin gargajiya a Najeriya ya rasu, Atiku da gwamna Mbah sun yi ta'aziyya

Za a fara dawo da mahajjatan Najeriya
Za a fara dawo da mahajjatan Najeriya daga Saudiyya. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa shugaban NAHCON ya taya mahajjata murnar kammala aikin Hajji, musamman wadanda suka halarci Arafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a fara dawo da mahajjatan jihohi 4

Farfesa Usman ya bayyana cewa jiragen farko da za su fara jigilar mahajjata sun hada da Air Peace daga jihar Imo, Max Air daga Bauchi da Flynas daga jihohin Kebbi da Sokoto.

Ya bukaci mahajjatan da ke cikin rukunin farko da su fara shiri tun daga yanzu, domin tafiyar dawowa gida ta kasance cikin tsari da kwanciyar hankali.

Ya kuma yi addu’a cewa Allah ya sauƙaƙa dawowar dukkan mahajjata zuwa gida lafiya, tare da fatan za su ci gaba da amfani da darussan aikin Hajji a rayuwarsu ta yau da kullum.

NAHCON ta gode wa hukumomi da ma’aikata

Hukumar ta yabawa kokarin hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi bisa jajircewa da tsari da suka nuna tun daga fara shirin hajjin bana har zuwa lokacin da mahajjatan suka kammala ibada.

Kara karanta wannan

Hajjin 2025: Mahajjaci ɗan Najeriya ya rasu a wuri mai daraja da albarka a Saudiyya

Farfesa Usman ya kuma jinjina wa ma’aikatan NAHCON da suka gudanar da ayyuka har cikin yanayin ihrami, yana mai cewa Allah ne zai saka musu da sakamako mafi alheri.

Ya kuma bayyana godiyarsa ga mambobin hukumar da ma’aikatan wucin gadi, bisa irin juriya da ƙwazo da suka nuna wajen hidimar “baƙin Allah” a ƙasa mai tsarki.

NAHCON ta yaba wa Shettima
NAHCON ta yaba wa shugaba Tinubu da Shettima. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

NAHCON ta yaba wa Tinubu da Shettima

NAHCON ta ce ba za ta iya mantawa da rawar gani da shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima suka taka ba wajen ganin ayyukan Hajji sun gudana ba tare da cikas ba.

Vanguard ta rahoto cewa Farfesa Fakistan ya bayyana cewa goyon bayan da gwamnatin tarayya ta bayar ne ya taimaka wajen ganin an gudanar da aikin hajji cikin nasara da tsari.

Limamin Arafa ya ja hankalin mahajjata

A wani rahoton, kun ji cewa limamin Arafa na 2025, Sheikh Abdallah bin Saleh Al Humaid ya yi kira ga mahajjata a Hajjin bana.

Limamin ya bukaci kowane mahajjaci da ya yi addu'a ga dukkan musulmai domin samun tsira a duniya da lahira.

Sheikh Abdallah bin Saleh Al Humaid ya bayyana wa mahajjatan matakan da za su bi wajen samun tsira a nan duniya da gobe kiyama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng