Borno: Sojoji Sun Kashe Boko Haram Suna Shirin kai Hari kan Masu Bikin Sallah

Borno: Sojoji Sun Kashe Boko Haram Suna Shirin kai Hari kan Masu Bikin Sallah

  • Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta kai wa ‘yan ta’adda farmaki a jihar Borno a ranakun 5 da 6 ga Yuni, 2025
  • An kai harin ne a daidai lokacin da ake zargin ‘yan ta’addan na shirin kawo cikas ga shagulgulan Sallah a Arewa maso Gabas
  • An kashe ‘yan ta’adda da dama tare da lalata sansanoni da cibiyoyin ajiyar kayayyakinsu a yankin Tumbumma da Chiralia

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta kai jerin hare-haren sama a jihar Borno domin dakile wani shiri na ‘yan ta’adda da ke kokarin kawo cikas ga bikin Babbar Sallah.

Hare-haren da aka kaddamar a ranakun 5 da 6 ga Yuni, 2025 sun mayar da hankali kan maboyar Boko Haram a Tumbumma Baba da Chiralia a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Yadda dakarun sojin Najeriya suka yi bikin sallah a fagen daga a Borno

Jirgin yaki ya saki wuta kan Boko Haram.
Sojoji sun kai hari kan Boko Haram suna kokarin farmakar masu shirin sallah. Hoto: @NigAirForce
Source: Getty Images

Rundunar sojin saman Najeriya ce ta sanar da nasarar da ta samu a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da inda ‘yan ta’addan ke buya da ajiye kayayyaki da kuma tsara hare-hare.

Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram a Borno

Rundunar sojojin ta ce hare-haren sun biyo bayan bayanan leƙen asiri ne da suka nuna cewa ‘yan ta’addan na amfani da wuraren da aka kai hari wajen ajiye makamai da shirya dabarun farmaki.

An bayyana cewa jiragen yaki sun yi ruwan bama-bamai kai tsaye kan sansanonin, inda suka tarwatsa shirin da Boko Haram ke yi domin hana zaman lafiya yayin Sallah.

An lalata sansanoni da kayan Boko Haram

Bayanai daga fannin tantance barnar da aka yi sun nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama a harin, tare da lalata manyan kayayyakin su na sufuri.

Kara karanta wannan

DSS da sojoji sun tarfa yaran 'dan ta'adda, sun aika mayakan Dogo Gide 45 barzahu

Hare-haren sun kuma shafi wuraren da ake zargin ana amfani da su wajen shirya dabarun ta’addanci da isar da sakonni tsakanin bangarorin ‘yan ta’adda.

Sojoji sun kai hari kan Boko Haram
An kashe maharan Boko Haram a jihar Borno. Hoto: Defence Headquaters
Source: Facebook

Sojin sama na sadaukarwa ga tsaron ƙasa

A cewar sanarwar da Daraktan Hulɗa da Jama’a na NAF, Ehimen Ejodame ya fitar, matakin ya nuna yadda sojojin sama ke da kwazo da sadaukarwa wajen kare rayukan fararen hula.

Ehimen Ejodame ya kara da cewa farmakin ya kara fito da kokarin dakarun soji na tabbatar da tsaron ƙasa.

Sanarwar ta kara da cewa nasarar harin ta sake bayyanawa duniya irin kokarin rundunar wajen wanzar da zaman lafiya da rushe hanyar sadarwa da sufuri na ‘yan ta’adda.

Sojojin sama sun yi bikin sallah a Maiduguri

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin saman Najeriya sun yi bikin sallah a birnin Maiduguri na jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban sojin saman ya yaba da kokarin da dakarun ke yi na yaki da 'yan ta'adda.

A hotunan da Legit ta tattaro na wajen taron, an hango sojojin suna cin abinci da shan abubuwan sha a wasu rumfuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng