Sabuwar Rigima Ta Kunno Kai a Masarautar Zazzau, Majalisa Ta Samu Korafin Tsige Sarki

Sabuwar Rigima Ta Kunno Kai a Masarautar Zazzau, Majalisa Ta Samu Korafin Tsige Sarki

  • Rikici ya sake kunno kai a masarautar Zazzau bayan majalisar dokokin Kaduna ta karɓi ƙorafin cire Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli
  • Tsohon Waziri, Ibrahim Muhammad-Aminu, ya zargi Nasir El-Rufai da sabawa doka da al’ada wajen nada Bamalli ba tare da bin tsarin masarauta ba
  • Ibrahim ya roƙi majalisa ta dawo da shi matsayinsa, ta soke nadin Bamalli kuma ta biya shi duk hakkokinsa da aka dakatar da su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Zazzau, Kaduna - Sabuwar rigima ta sake kunno kai a masarautar Zazzau da ke jihar Kaduna a Arewacin Najeriya.

Tsohon Wazirin Zazzau, Ibrahim Muhammad-Aminu, ya kai ƙorafi ga majalisar dokokin jihar Kaduna yana neman a soke nadin Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli.

Ana neman tsige Sarkin Zazzau
An kai wa majalisa korafi dokin tsige Sarkin Zazzau. Hoto: Masarautar Zazzau.
Source: Facebook

Tsohon Wazirin Zazzau ya yi korafi a majalisa

Hakan na cikin ƙorafin da ya aike wa kakakin majalisar Yusuf Dahiru-Liman, wanda jaridar Daily Nigerian ta samu.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista kuma ƙwararren likita, Farfesa Jibril Aminu ya kwanta dama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin korafin, ya zargi tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da karya doka wajen nadin Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau da ke Arewacin Najeriya.

Ibrahim ya ce an yi watsi da zaɓen da masu nadin sarki suka yi, wanda aka gudanar bisa al’ada da dokokin masarautar Zazzau.

A cewarsa, wadanda masu zaɓe suka gabatar su ne: Alhaji Bashir Aminu, Alhaji Muhammad Munir Ja’afaru da Aminu Shehu Idris.

"Ambasada Ahmad Bamalli bai cikin jerin sunayen da aka miƙa wa gwamnati, kuma nadinsa ya saba wa doka da al’ada."

- A cewarsa

Tsohon Wazirin Zazzau ya yi korafi kan sarauta
Rigimar sarautar Zazzau ta dawo sabuwa. Hoto: Masarautar Zazzau.
Source: Facebook

Zarge-zargen da tsohon Wazirin Zazzau ya gabatar

Ibrahim ya kara da cewa an tsige shi ba bisa ka’ida ba daga matsayin Waziri, an kama shi kuma aka gurfanar da shi babu dalili.

Tsohon Wazirin ya ce wani mutum mai suna Alhaji Inuwa Aminu ne aka maye gurbinsa da shi bai cancanci hakan ba.

Ya roƙi majalisar ta soke nadin Sarkin Zazzau, ta dawo da shi matsayin Waziri, ta biya shi dukkan hakkokinsa da aka dakatar da su, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Sarkin Musulmi ya yi kira ga 'yan Najeriya game da ranar Arafa

Yadda ake zargin nada Sarki babu ka'ida

Ya ce nadin da aka yi ya sabawa kundin tsarin mulki na Kaduna mai lamba. 9 Vol. 54 na 7 ga watan Oktobar 2020 da al’adun masarautar Zazzau.

Ya kara da cewa:

"Tunani ne na dawo da adalci da mutunta al’ada da tsarin masarautu na Arewacin Najeriya duba muhimmanci da suke da ita."

Kotu ta yi hukunci kan rigimar masarautar Zazzau

Mun ba ku labarin cewa kotun daukaka kara da ke Kaduna ta yi watsi da karar da ke neman tsige Sarkin Zazzau na 19, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.

Tubabben Wazirin Zazzau, Ibrahim Mohammed Aminu, shi ya kai karar bisa zargin rashin bin doka wajen nadin sarkin da aka yi masa a matsayin Sarki.

Kotun ta bayyana cewa karar ba ta da inganci don haka ba za a ci gaba da sauraren ta ba, kuma ta ce babu uzuri duba da yanayi da lokacin da aka shigar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.