Shari'ar nadin Sarkin Zazzau, artabun da aka yi a kotu tsakanin Iyan Zazzau da sauran wadanda ake kara

Shari'ar nadin Sarkin Zazzau, artabun da aka yi a kotu tsakanin Iyan Zazzau da sauran wadanda ake kara

- Alkalin wata babban kotun da ke zama a Zaria, jihar Kaduna ya dage shari'ar nadin sarkin Zazzau zuwa ranar 2 ga Nuwamba

- A yayin shari'ar, lauyan gwamnatin jihar ya kalubalanci ikon kotun na sauraron shari'ar a suka ta farko

- Amma mai kara, Iyan Zazzau ya bukaci kotun da ta hana gwamnan Kaduna mu'amala da wani a matsayin Sarkin Zazzau har sai an kammala shari'ar

Alkali Kabir Dabo na jihar Kaduna, wanda ke zama a babbar kotun Zaria, ya daga shari'ar zuwa 2 ga watan Nuwamba, don jin sukar farko da gwamnatin jihar Kaduna zatayi akan ikon kotu wurin zaben sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli.

Bayan sauraron shari'ar a ranar Talata, lauyan gwamnatin jihar, Sunusi Usman, ya kalubalanci ikon kotun wurin sauraro da yanke hukunci.

Usman, wanda shine shugaban lauyoyin gwamnatin jihar, ya sanar da kotu cewa ya rubuto duk kalubalen da yake da su a kan hukuncin kotun a ranar 26 ga watan Oktoba, kuma ya kawo wa wadanda yake kara a ranar 27 ga watan Oktoba.

Lauya mai kare wadanda ake kara, Yunus Usman, SAN, ya roki kotu da ta bayar da damar jin ta bakin bangarori biyu kafin ta yanke hukunci, Daily Nigerian ta wallafa.

Idan ba a manta ba, an yi wancan zaman kotun a ranar 19 ga watan Oktoba, Alkalin ya umarci duk wadanda ake kara a mika musu sammaci.

Kamar yadda Bashir Aminu, wanda ke kara ya bukaci kotun, ya roketa da ta hana gwamnan jihar Kaduna wata mu'amala ko kiran wani sarkin Zazzau har sai lokacin da aka kammala shari'ar.

KU KARANTA: Wawushe dukiyoyin jama'a : 'Yan sanda sun damke mutum 224 a jihohi Kwara da Cross River

Shari'ar nadin Sarkin Zazzau, artabun da aka yi a kotu tsakanin Iyan Zazzau da sauran wadanda ake kara
Shari'ar nadin Sarkin Zazzau, artabun da aka yi a kotu tsakanin Iyan Zazzau da sauran wadanda ake kara. Hoto daga @GovKaduna
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Matasa sun banka wa gidan rediyo wuta a jihar Taraba

A wani labari na daban, Teslim Folarin, dan majalisa mai wakiltar mazabar Oyo ta tsakiya, ya ce karnukansa duk suna cikin keji ne, lamarin da yasa basu yagalgala naman wadanda suka kai farmaki gidansa ba a ranar Asabar.

Fiye da babura 250, firji 400, janareto 35 aka kwashe a gidan sanatan wadanda aka ware domin karfafa matasa a mazabarsa.

A tattaunawar da yayi da Dele Momodu a ranar Lahadi, Folarin ya bayyana mamakinsa a kan wannan harin, The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel