Ma'aikatan Wuta Sun Yi Gargadi, Ana Shirin Jefa Abuja da Wasu Jihohi 3 a cikin Duhu
- Kungiyoyin ma’aikatan wuta sun ce za su koma yajin aiki domin sake tunawa kamfanin rarraba wuta na Abuja yarjejeniyarsu
- Kungiyoyin NUEE da SSAEAC ne za su tafi yajin aikin bayan sun zargi kamfanin AEDC da gaza mutunta yarjejeniyar da aka cimma
- Ma’aikatan sun fitar da korafe-korafe da suka hada da rashin fansho, rashin karin girma da kin biyan mafi karancin albashi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Za a iya fuskantar matsalar wutar lantarki a Abuja, da wasu jihohi bayan kungiyoyin ma’aikatan wutar lantarki sun bayyana shirinsu na komawa yajin aiki.
Ma’aikatan na kungiyoyin ma'aikatan wutar lantarki na kasa (NUEE) da manyan ma'aikatan bangaren lantarki da kamfanoni (SSAEAC), sun ce za su tafi yajin aiki babu sanarwa.

Kara karanta wannan
Bayan ganawa da wakilan gwamnati, ma'aikatan shari'a sun amince a janye yajin aiki

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa ma'aikatan na son tafiya yajin aikin ne sakamakon gazawar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) wajen cika yarjejeniyar da suka cimma a shekarar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin AEDC, shi ne ke da alhakin rarraba wutar lantarki a Abuja da jihohin Neja, Nasarawa da Kogi.
Dalilin ma’aikatan wuta na fara yajin aiki
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kungiyoyin sun aika da wasiku daban-daban zuwa ga Darakta Janar na AEDC, inda suka ce ba za su sake bata lokaci ba kafin fara yajin aikin.
A cikin wasikar, kungiyoyin sun tuna wa AEDC cewa an cimma yarjejeniya da su ranar 27 ga Nuwamba, 2024, domin dakatar da yajin aiki da aka fara bisa rikici kan kwadago a kamfanin.

Source: Getty Images
Wasikar ta ce:
“Abubuwan da muke korafi a kansu sun hada da: Rashin biyan kudin fansho da aka cire tsawon watanni 16, rashin aiwatar da mafi karancin albashi, rashin kara wa ma’aikata girma na fiye da shekara 10, rashin tabbatar da wadanda ke aiki na wucin gadi, da kuma kin mayar da ma’aikatan wucin gadi zuwa ma’aikatan dindindin.”
Ma’aikatan wutan lantarki sun fusata
Ma’aikatan sun bayyana cewa duk da gazawar kamfanin wajen cika alkawura da kayan aiki masu kyau, sun samar da kudin shiga har Naira biliyan 94 a cikin kwanaki 90 da suka gabata.
Kungiyoyin sun kara da cewa:
“Muna sanar da ku cewa za mu cigaba da yajin aikin da muka dakatar daga ranar 27 ga Nuwamba, kuma za mu iya fara wa tun daga lokacin da kuka karɓi wannan wasika ba tare da wani karin gargadi ba.”
Yajin aikin na iya haifar da karancin lantarki a Abuja, Kogi, Neja da Nasarawa, yayin da shugabannin kungiyar suka umarci 'ya'yansu da su kwana a cikin shiri.
Sojoji sun yiwa ma'aikata wutar lantarki duka
A wani labarin, mun wallafa cewa wasu sojoji sun lakadawa ma’aikatan kamfanin rarraba wutar lantarki duka a Abuja, bayan yanke musu wuta a barikin su da ke Asokoro.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 30 ga Mayu, 2024, lokacin da ma’aikatan wutar suka je duba wani aiki a yankin, bayan an yanke wuta daga ofishin su na kamfanin rarraba wuta dake Abuja.
Rahotanni sun ce ma’aikatan sun je gyaran wani layin lantarki da ya shafi barikin sojojin, amma da isarsu wajen, sai wasu sojoji suka tare su, suka zarge su da yanke wutar da gangan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
