Muhimman Abubuwa 5 da Ya Kamata Musulmi Ya Yi a Ranar Arafah
- Ranar Arafah na daya daga cikin ranaku mafi albarka a Musulunci, ana yin azumi da addu’o’i domin samun gafara da rahamar Allah SWT
- A wani hadisi, Annabi Muhammad (SAW) ya ce azumin ranar Arafah yana goge zunuban shekarar baya da ta gaba
- Ana son Musulmi su tashi kafin asuba su yi Tahajjud da addu’a, haka nan, a fara shirye-shiryen layya domin cika wannan ibada mai girma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ranar Arafah, wadda take rana ta 9 ga watan Dhul Hijjah, na daya daga cikin mafiya tsarki a Musulunci, tana ba da dama ga ibada da neman gafara.
Musulmi a fadin duniya, ko suna aikin Hajji ko a’a, suna keɓe wannan rana don addu’a da ambaton Allah domin neman rahama da albarka.

Source: Twitter
Muhimman abubuwa da ake yi a ranar Arafah
Akwai muhimman abubuwa guda biyar da ya dace a yi domin samun lada mai yawa a wannan rana mai albarka da kusanci da Allah, cewar rahoton Islamic Relief UK.
A ranar Arafah mahajjata suna tsayawa a filin Arafah suna addu’a da neman rahamar Allah, wadanda ba su yi Hajji ba su kara yawaita ibada da neman gafara.
Legit Hausa ta duba jerin abubuwan da ya kamata a yi a ranar Arafah:
1. Azumi a ranar Arafah
Azumi a ranar Arfah Sunnah ne mai karfi ga wadanda ba su yin Hajji. Annabi Muhammad (SAW) ya ce:
“Azumin ranar Arfah yana goge zunuban shekara da ta gabata da kuma ta gaba."
Wannan ibada na daga cikin hanyoyin samun yardar Allah da gafararsa, wanda ya yi azumi a wannan rana yana samun rahamar Allah SWT, komai yawan zunubansa.
2. Yin addu’a da neman gafara
Ranar Arfah dama ce ta musamman wajen addu’a, Annabi Muhammad (SAW) ya ce a hadisin Tirmidhi:
“Mafi kyawun addu’a ita ce ta ranar Arfah."
Haka kuma, Allah ya yi umarni a cikin Alkur’ani:

Kara karanta wannan
Ta'addanci: Jagororin Fulani sun nemi a tattauna, an sako Turji cikin masu neman sulhu
"Ku ambaci Allah a cikin kwanaki da aka kayyade.” — Surar Al-Baqarah | 2:203
Ana son Musulmi su ware lokaci don addu’a mai yawa, neman rahama, shiriya da gafarar Allah.

Source: Getty Images
3. Yawaita zikiri da ibada ranar Arafah
Ambaton Allah da zikiri yana da matukar muhimmanci a wannan rana, mafi kyawun nau’in zikiri sun hada da:
Zikiri (Laa ilaaha il-lal-laah)
Kabbara (Allahu Akbar)
Godiya (Alhamdulillaah)
Tasbihi (Subhanallaah)
Sunnah ce a yawaita fadar wadannan a ranar Arafah, idin babbar sallah da kwanaki masu zuwa na Dhul Hijjah.
Musulmi su yawaita karatun Alkur’ani, sallolin Nafila da salati ga Annabi (SAW), cewar rahoton Muslim Aid.
4. Shirin layya
Ko da yake ana yanka layya daga 10 zuwa 12 ga Dhul Hijjah, ana fara shiri tun ranar Arafah.
A cewar Mazhabin Hanafi, layya wajibi ne ga baligi, mai hankali wanda ke da dukiya fiye da bukatunsa na yau da kullum.
Abu Dawud ya ruwaito:
“Annabi ya yanka hadaya a Ranar Hadaya. Ya ce: ‘Na juya fuskata ga mahaliccin sammai da kasa, akan addinin Ibrahim, ina bauta wa Allah kaɗai… Lallai salla ta, da ibada ta, da rayuwa ta da mutuwa ta, duk domin Allah Ubangijin Halittu ne.’”
Musulmi su tabbata sun shirya hadayarsu kafin idi don cika wannan ibada mai daraja.

Source: Original
5. Tashi kafin asuba domin tahajjud
Wani lokaci mai albarka shi ne kashi na karshe na dare, Annabi Muhammad (SAW) ya ce:
“An tambaye shi wane addu’a ne ake amsawa, sai ya ce: ‘A cikin kashi na karshe na dare, da bayan sallolin farilla.’” — Hadisi | Tirmidhi, 3499
Ana son Musulmi su tashi kafin asuba su ci sahur su kuma yi sallar Tahajjud. Wannan lokaci ne da ya dace wajen neman rahama da gafarar Allah ta hanyar addu’a mai tsanani.
Dokokin ranar Arafah
Mahajjata ba su yin azumi a wannan rana, suna zuwa filin Arafah, suna tsayuwa har zuwa faduwar rana, suna fuskantar alkibla da addu’a na neman gafara.
Annabi (SAW) ya ce:
“Hajji shi ne Arafah.”
Ga wadanda ba sa Hajji, azumi yana da matukar lada kuma Sunnah ne, Musulmi su yi amfani da wannan rana wajen yawaita ibada da neman rahamar Allah.
Ta hanyar aiwatar da wadannan abubuwa guda biyar, Musulmi za su kara kusanci da Allah da kuma shiri don albarkar idin babbar sallah.
Saudiyya ta hana ɗaukar hotuna yayin ibada
Mun ba ku labarin cewa hukumomi a ƙasar Saudiyya ta hana daukar hoto da rera wakoki ko daga tutoci a wuraren ibada yayin aikin Hajji.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce haramun ne yin hoto da waya ko kayan daukar hoto a Masallacin Harami, Madina, Mina, Arafat da kuma Muzdalifa
Gwamnatin kasar Saudiyya ta ce aikin Hajji lokaci ne na ibada da hadin kai, kuma za a hukunta duk wanda ya karya doka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


