Zauren Musulunci: Falalar Ranar Arafah
- Ranar 9 ga wannan wata ce Ranar nan ta Arafah a Addinin Musulunci
- Allah Madaukaki ya rantse da ranakun Watan da kuma ta Ranar Arafah
- Ana karbar addua da kuma 'yanta bayin Allah a wannan Rana ta musamman
A cikin al kurani Ubangiji ya rantse da wannan rana ta Arafah da ake taruwa na musamman a Suratul Buruj.
Daga cikin darajar wannan rana akwai cewa:
1. A wannan rana ne aka cika sakon Addinin Musulunci inda har Aya ta sauka a cikin Suratul Ma'ida
KU KARANTA: Saudiyya ta hana mahajjata da dama shiga kasar saboda rashin takardu
2. Kuma a wannan rana ne ake 'yanta bayin Allah da dama kamar yadda Hadisi ya zo a littafin Sahih Muslim
3. Har wa yau kuma babu ranar da Ubangiji yake karbar addua kamar wannan rana wanda shi ma ya zo a littafin Silsilal hadith na Sheikh Nasir Deen Albany.
Duk wani Mahajjaci a wannan rana ya dukafa ana kuma neman rahamar Allah. Ana son azumi ga wadanda ba su je Hajji ba wanda ke kankare zunuban shekara biyu. Azumin ranar Arafah na yafe zunuban shekarar bara da kuma shekarar bana da ake ciki inji Manzon Allah SAW.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Dubi yadda ake cinikin raguna na bikin idi
Asali: Legit.ng