Bayan Sanarwar Sanusi II, Aminu Ado Ya Dakatar da Hawan Sallah a Kano
- Alhaji Aminu Ado Bayero ya dakatar da duk wani shirin haye-haye da ake yi a lokutan bukukuwan Sallah a shekarar 2025
- An dauki matakin ne bayan shawarar da aka yi da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin Kano
- Mai martaban ya ce zaman lafiya da tsaron jama’a ya fi komai muhimmanci a wannan lokaci da ake fuskantar kalubalen tsaro
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Mai martaba sarki Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayar da umarnin dakatar da hawan Sallah.
Wannan matakin na zuwa ne sakamakon tattaunawa da hukumomin tsaro da kuma duba halin da ake ciki a jihar Kano da kasa baki daya.

Source: Facebook
Legit ta gano bayanin da Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi ne a cikin wani sako da shafin masarautar Kano ta wallafa a X.

Kara karanta wannan
Gwamna Bago ya bi sahun ƴan sandan Kano, ya hana hawan Sallah saboda abin da ya faru
Dalilin dakatar da hawan sallah a Kano
Sakataren Majalisar Masarautar Kano bangaren Aminu Ado Bayero, Auwalu Abbas Sanusi ya fitar da sanarwa kan dakatar da hawan sallah a Kano.
A cewar sanarwar, Mai martaba Aminu Ado ya dauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da guje wa duk wata barazana ga jama’a da jihar Kano gaba daya.
Masarautar ta ce duba da yadda al’amura ke tafiya da hadarin da ya jawo mutuwar 'yan wasan Kano, da shawarar hukumomin tsaro, an ga dacewar a dakatar da hawan a bana.
Aminu Ado ya ce tsaro da doka sun fi al’ada
Fadar Masarautar ta bayyana cewa ana bukatar jama’a su rungumi zaman lafiya da biyayya ga doka fiye da komai.
Sanarwar ta ce doka da oda sun fi muhimmanci a halin yanzu fiye da al’adar haye-haye da ake yi a lokacin bukukuwa.

Source: Twitter
Mai martaba Aminu Ado Bayero ya ce yana da kyau a kaucewa duk wani abu da zai iya kawo rashin zaman lafiya ko tayar da hankali.

Kara karanta wannan
Sallah: Sarki Sanusi II ya fitar da sanarwar shirin hawa a Kano, ya umarci hakimai
Sarki ya bukaci a kula da yara a lokaci sallah
Mai martaban ya bukaci iyaye da su kula da ‘ya’yansu, su guji shiga duk wata harkar da za ta janyo fitina ko tayar da hankali.
A cewar masarautar, doka da oda na cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwar al’umma, don haka ne sarkin ya bukaci a dakatar da haye-haye har zuwa wani lokaci da za a ga ya dace.
A karshe, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga daukacin al’umma da su ci gaba da addu’a da godiya ga Allah, musamman lura da nasarorin da suke cigaba da samu.
Sanusi II ya fitar da sanarwa kan hawan sallah
A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II ya fitar da sanarwa kan hawan sallah a jihar Kano.
Mai martaba sarkin ya umarci dukkan masu rike da sarauta da su shirya domin gudanar da hawan sallah a jihar.
A karamar sallah da ta gabata ma dai sarkin ya fitar da sanarwa kan hawan sallah amma daga baya 'yan sanda suka dakatar da bikin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng