Kwana Ya Kare: Almajirai 11 Sun Rasu daga zuwa Taimakon Malaminsu a Jihar Kaduna
- Wasu almajirai 11 sun rasa rayukansu a wata mahaƙar ƙasa da ke kauyen Yar-doka a ƙaramar hukumar Kubau ta jihar Kaduna
- Rahotanni sun bayyana cewa almajiran sun je wurin ne da nufin taimakon malaminsu, kwatsam ƙasa ta rufa kansu ranar Litinin
- Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an tura jami'ai domin fara bincike kan haƙiƙanin abin da ya afku
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Wasu ɗalibai da ke karatun Alƙur'ani waɗanda aka fi sani da almajirai har 11 sun rasa rayukansu a ramin da ake haƙo ƙasar bulo a jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ƴar-doka da ke yankin ƙaramar hukumar Kubau ranar Litinin da ta gabata da misalin ƙarfe 1:45 na rana.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa almajiran sun je wurin ne domin taimaka wa malaminsu wajen yin bulon da za a yi ginin laka, kwatsam zato ƙasa ta rufto kansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Almajirai 11 sun mutu a rami a Kaduna
Wadanda suka rasu, masu shekaru tsakanin 10 zuwa 15, sun hada da, Muntari Abdulkadir, Aliyu Abba, Ali Umar, Mubarak Haruna, Usain Isa, da Yusuf Shafiu.
Sauran sun haɗa da Mujitafa Jibril, Yusha’u Saidu, Aliyu Abdu, Hamisu Mohammed, da Ali Abdulmomini.
Duka almajiran da lamarin ya shafa 'yan asalin kauyen Yar-doka ne da wasu makwaftan garuruwan da ke cikin yankin Damau.
A rahoton da Vanguard ta kawo, ta ce jama'a sun ceto wasu yaran guda bakwai da suka samu raunuka iri daban-daban a ramin haƙo ƙasar bulon.
Waɗanda suka samu raunukan sune, Umar Dini, Jibir Surajo, Usman Abdulmomini, Sagir Hussaini, Naziru Abdullahi, Aminu Alkasim, da Kabiru Lawal.
Bayanai daga mazauna yankin sun nuna cewa an garzaya da su asibitin kula da lafiya na farko da ke Yardoka, inda suke karbar kulawa a halin yanzu.
Me ya kai almajiran cikin ramin?
Wani dagaci a yankin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce:

Kara karanta wannan
Bayan ganawa da wakilan gwamnati, ma'aikatan shari'a sun amince a janye yajin aiki
"Eh, lamarin ya faru ne da tsakar rana a ranar Litinin. Yara 11 sun mutu, yayin da aka kai wasu shida asibiti saboda raunukan da suka samu.
"Tara daga cikin wadanda suka mutu ba 'yan Yar-doka ba ne, almajirai ne da da suka zo tare da malaminsu suna karatu.
"Ba bulon sayarwa suka je yi ba, wannan wuri dai an saba amfani da shi wajen hako ƙasa domin gine-gine ko gyaran gida.”
Wani mazaunin yankin mai suna Usman ya bayyana lamarin a matsayin jarabawa da ta girgiza jama’a.

Source: Twitter
Ƴan sandan Kaduna sun fara bincike
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana cewa jami’ai sun garzaya zuwa wurin da hatsarin ya faru bayan samun kiran gaggawa.
Ya kara da cewa tuni aka kaddamar da bincike domin gano hakikanin dalilin aukuwar wannan mummunan lamari.
Kaduna da wasu jihohi na fuskantar haɗari
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NiMet ta gargaɗi jihar Kaduna da wasu jihohi kan yiwuwar ambaliya a watan Yuni.
NiMet ta yi hasashen saukar ruwan sama mai karfi da yiwuwar ambaliya a jihohi da dama musamman a Arewacin Najeriya.
Jihohin da hukumar ta ce za a iya yin ambaliya sun haɗa da Kano, Kaduna, Neja, Nasarawa, Kwara, Sokoto ta Filato, tana mai cewa za a yi ruwan sama mai ƙarfi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

