Ta'addanci: Jagororin Fulani Sun Nemi a Tattauna, an Sako Turji cikin Masu Neman Sulhu

Ta'addanci: Jagororin Fulani Sun Nemi a Tattauna, an Sako Turji cikin Masu Neman Sulhu

  • Shugabannin Fulani a Zamfara sun koka kan yadda ake nuna musu wariya da zalunci, sun ce ba su duka ba ne ‘yan ta’adda ba
  • A wani taron wayar da kai a Gusau, shugabannin Fulani sun bayyana damuwarsu, suka ce rashin adalci ke tura matasa shiga ta’addanci
  • Wasu fitattun shugabannin miyagun ‘yan bindiga sun bayyana shirin su na mika wuya matukar gwamnati ta ba su tabbacin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - A cikin dazukan jihar Zamfara da ke fama da rikici, wasu daga cikin Fulani makiyaya na neman zaman lafiya ta hanyar adalci da tattaunawa.

Sun ce za su rungumi zaman lafiya idan gwamnati ta warware matsalolin da suka jima suna fuskanta, waɗanda suka haddasa rikice-rikice masu yawa.

Turji na daga cikin masu neman sulhu
Shugabannin Fulani sun koka kan rashin adalci a Zamfara. Hoto: Legit.
Source: Original

Ta'addanci: An yi taron sulhu a Zamfara

Kara karanta wannan

Sanata ya fadi yadda ake kara karfin Boko Haram don dagula mulkin Tinubu

Tsawon shekaru akalla 10 Arewa maso Yammacin Najeriya na fama da ta’addanci, satar shanu da hare-hare na ramuwar gayya da suka hallaka dubban mutane, cewar Zagazola Makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai a wani taron musamman da aka yi a Gusau, shugabannin Fulani sun nuna aniyar su na barin tashin hankali muddin an yi musu adalci.

Wannan taron wayar da kai da aka gudanar ranar 4 ga Mayun 2025 ya haɗa manyan jami’an tsaro da shugabannin MACBAN daga kananan hukumomi 14.

A taron ne shugabannin Fulani suka bayyana matsalolin da suka dade suna fuskanta tare da neman goyon bayan gwamnati ta hanyar adalci.

Suka ce:

“Ba dukan mu ne ‘yan bindiga ba."

Har ila yau, wani Fulani ya bayyana cewa bai taba rike ko makami ba amma yan sa-kai sun sace masa shanu fiye da 150.

“Ina da shanu fiye da 150 da yan sa-kai suka kwace, amma ban taɓa ɗaukar makami ko shiga wata ƙungiya ba."

- Cewar Malam Salisu Umar

Yadda ake sace shanun Fulani a Zamfara

Wani makiyayi, Muhammadu Sale, ya ce yan sa-kai sun sace shanu kusan 300 na wani Fulani mai bin doka, suka sayar a kasuwa ba tare da hukunci ba.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Buhari ya girgiza da mutuwar mutane kusan 200 a Kano da Neja

Wasu da dama a taron sun bayyana yadda ake kama matasa Fulani, a dake su har su amsa laifin cewa su ‘yan ta’adda ne sannan a kashe su babu shari’a.

Alhaji Musa Bature daga Tsafe ya zargi jami’an tsaro da haɗin gwiwa da yan sa-kai wajen sace shanu da sayar da su a kasuwa.

Ya ce wannan rashin adalci yana tura matasa Fulani shiga ta’addanci, sun ce yunwa da tsadar abinci ke tilasta su aikata laifi.

Umar Jega daga Bakura ya ce an kone garinsu gaba ɗaya a bara, amma ba a hukunta kowa ba, ya ce ana kallonsu kamar ba su da ‘yanci.

Shugabanni da dama sun danganta shigar matasa Fulani ta’addanci da rashin adalcin da suke fuskanta daga hukumomi da wasu kungiyoyi.

Shugabannin Fulani sun nemi adalci a Zamfara
Bello Turji na daga cikin masu neman a yi sulhu a Zamfara. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Source: Facebook

Wasu fitattun ‘yan bindiga na shirin mika wuya

Wasu fitattun shugabannin ‘yan bindiga sun bayyana niyyar su na ajiye makamansu idan an ba su tabbacin tsaro da sake komawa rayuwa cikin al'umma.

Saidu Naeka, Jimmi Smally, Kabiru Yankusa da wasu sun nuna sha’awar mika wuya, haka kuma, Bello Truji da Alhaji Nashama sun amince.

Wasu daga cikin su na jin tsoron wannan shirin da ake yi, suna ganin ana so a yaudare su ko kuma a kama su ta dabara.

Kara karanta wannan

'Yadda za mu kwace mulki daga hannun Tinubu a 2027,' Atiku, El Rufai sun magantu

Ado Aleiro da Madele suma sun tura wakilansu taron, aka bayyana cewa sun gaji da rikici, suna neman zaman lafiya da martaba.

'Yan bindiga sun sace masallata a Zamfara

Kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari cikin masallaci a Unguwar Galadunci da ke Anka a jihar Zamfara a farkon daminar shekarar nan.

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kai harin da dare yayin da ake tsuga ruwan sama a yankin.

'Yan bindigar sun sace wasu daga cikin masu ibada yayin sallar Ishai, inda wasu suka jikkata kamar yadda aka tabbatar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.