Gwamna Bago Ya Bi Sahun Ƴan Sandan Kano, Ya Hana Hawan Sallah saboda Abin da Ya Faru
- Muhammed Umaru Bago ya ba da umarnin taƙaita shagulgulan sallah saboda ibtila'in ambaliyar da ya faru a garin Mokwa da kewaye
- Gwamnan jihar Neja ya hana hawan sallah da duk wani nau'in hawa da bukukuwan sallah da sarakuna ke yi a lokacin babbar sallah
- Sakataren gwamnatin Neja, Abubakar Usman, wanda ya isar da sakon gwamnan, ya ce an ɗauki matakin ne domin jimamin rasa mutanen Mokwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Gwamna Muhammed Umaru Bago ya ba da umarnin hana hawan bariki, hawan sallah da sauran bukukuwan sallah da ake shiryawa a duka masarautun jihar Neja.
Gwamna Bago ya buƙaci duka masarautu da sauran al'umma su yi haƙuri su taƙaita shagalin sallah duba da halin da jihar ta tsinci kanta a ciki.

Source: Facebook
Abin da ya jawo hana hawan sallah a Neja

Kara karanta wannan
Yadda aka zabga wa Sarki lafiyayyen mari a taron da gwamnan Ondo ya kaddamar da titi
Umaru Bago ya ɗauki wannan matakin ne sakamakin mummunar ambaliya da ta afku a Mokwa da kewaye, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaiito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ambaliyar ruwan wacce ta afku sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a daren ranar Laraba ta makon jiya, ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 200.
Haka nan rahotanni sun nuna cewa har yanzu ana neman mutane sama da 1000, sannan an yi asarar dukiyoyi da kadarori masu dumbin ya.
Gwamna Bago ya buƙaci taƙaita shagalin sallah
Domin nuna alhini da makokin abin da ya faru, Gwamna Bago ya ba da umarnin taƙaita shagulgulan sallah a faɗin jihar Neja, rahoton Daily Post.
Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Abubakar Usman, shi ne wanda ya isar da umarnin Gwamna Bago a wata sanarwa da ya fitar.
Ya bayyana cewa an yanke wannan shawarar ne a domin girmamawa ga wadanda abin ya shafa, da kuma ba da damar yin makoki, addu’a da nazari a kan wannan ibtila’in.

Source: Twitter
'Ambaliyar Mokwa ita ce mafi muni a Neja'
Sakataren gwamnatin ya kara da cewa ambaliyar da ta faru a Mokwa na daya daga cikin mafi muni da jihar ta fuskanta a tsawon shekaru masu yawa, inda iyalai suka rasa ‘yan uwa, gidaje da hanyoyin samun abin rayuwa.

Kara karanta wannan
Eid El Adha: 'Yan sanda sun sake cin karo da Sarki Sanusi II, an haramta hawan Sallah a Kano
Sakataren ya kuma isar da wannan sako ga duka masautun jihar Neja, yana mai cewa hakan zai ba ƴan uwan waɗanda aka rasa damar makokin ƴan uwansu.
Tsohon gwamna ya ba da tallafin N50m a Mokwa
A wani labarin, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Neja ta Arewa kuma shugaban kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawa, Abubakar Sani Bello ya yi alhinin ambaliyar da ta afku a Mokwa.
Sanatan, wanda tsohon gwamnan jihar Neja ne ya bayar da tallafin Naira miliyan 50 domin ragewa mutane raɗafin ambaliyar da ta yi ajalin mutane akalla 200 da lalata gidaje.
Abubakar Sani Bello ya kuma yi addu’ar samun rahamar Allah ga waɗanda suka rasa rayukansu da kuma samun addu'ar Allah Ya maida mafi alherin dukiyar da aka rasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng