Yadda Aka Zabga Wa Sarki Lafiyayyen Mari a Taron da Gwamnan Ondo Ya Kaddamar da Titi
- Faɗa ya kaure tsakanin wani Sarki da shugaban al'umma a wurin taron da aka shirya domin kaddamar da fara gina titi a Ondo
- Shaidu sun bayyana cewa wani mutumin ya naushi basaraken a kunne da baki, wanda ya sa aka garzaya da shi asibiti
- Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ne ya jagoranci taron kuma sarkin da aka ji wa raunin shi ne mai masaukin baki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ondo - Rahotanni sun nuna cewa faɗa ya kaure tsakanin wani shugaban al'umma da sarkin Igbokoda, Oba Odidiomo Afolabi, a wurin wani taro ranar Litinin a Ondo.
Lamarin ya faru ne a wurin wani taro da aka shirya a garin Igbokoda da ke yankin karamar hukumar Ilaje.

Source: Original
Daily Trust ta ce rikicin ya faru ne a lokacin bikin kaddamar da aikin gina titin Igbokoda zuwa Okitipupa mai tsawon kilomita 27.5, wanda Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya jagoranta.

Kara karanta wannan
"Shekara 8 ina matsayin gwamna amma ban samu komai ba," Kalu ya tuna abin da ya faru
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda faɗa ya kacame da Sarki a Ondo
Wani ganau ya ce faɗan ya samo asali ne daga sabani kan yadda aka tsara kujerun da shugabanni za su zauna kafin zuwan Gwamna Aiyedatiwa.
Sarki Odidiomo, wanda shi ne babban mai masaukin baƙi a taron, ya bukaci mutumin ya tashi ya bar kujerar gaba don a ba wa sarakunan wuri.
Sai dai majiyar ta ce mutumin ya ki bin umarnin sarkin, lamarin da ya fusata Oba Odidiomo kuma ya rikide zuwa fada da doke-doke.
A faɗan, an ce mutumin ya cire rawanin sarkin, ya kuma yaga masa rigar sarauta, kafin daga bisani ya naushe shi a kunne da haƙora, lamarin da ya sa aka garzaya da shi asibiti cikin jini.
An naushi Sarki har aka ji masa rauni
"Sarkin ya bukaci mutumin ya bar kujerar gaba domin kada ya hana sarakuna gani sosai, amma mutumin ya dauki lamarin da zafi.
"Ya fara zagin sarkin, sannan ya far masa, ya cire masa rawani da zobba. A lokacin da faɗan ya kaure ne ya naushi sarkin a kunne, aka dauke shi zuwa asibiti,” in ji ganau.
Saboda jin rauni, sarkin bai samu halartar taron ba duk da kuwa shi ne mai masaukin baki na musamman.

Source: Facebook
Matasa da mata sun ɓarke da zanga-zanga
Bayan faruwar lamarin, matasa da mata da dama, ciki har da wasu da suka fito tsirara, sun gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin jin daɗin abin da suka kira cin mutunci da tozarta al’ada.
Sun bukaci hukumomi su dauki mataki, inda suka bayyana lamarin a matsayin “cin mutuncin al’adun gargajiya” kuma abin kunya ga masarautarsu.
Da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Mr Olusola Ayanlade, ya bayyana cewa ba a kai rahoto ga ofishinsu ba.
"Ba a kawo rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda ba,” in ji shi.
Sarki ya bulale mutanensa a jihar Ondo
A wani labarin, kun ji cewa an gurfanar da wani basarake a jihar Ondo mai suna Ojo Olomolekulo gaban wata kotun majistare a Akure bisa tuhumar cin mutuncin jama'arsa.

Kara karanta wannan
Ambaliya: Sheikh Pantami ya yi magana kan mutuwar mutane sama da 100 a Jihar Neja
Ana zargin Sarkin ya haɗa kai da wasu mutane, sun lakaɗawa mutanen yankinsa suka saboda sun ki biyan harajin da ya sanya masu.
Haka zalika, ana zargin Ojo Olomolekulo da sayar da wani yanki na dajin gwamnati ga wasu mutane biyu ba bisa ƙa'ida ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
