Shehu Sani Ya Fadi Mutum 2 da Suka Assasa Matsalar 'Yan Bindiga da Yunwa a Najeriya
- Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya caccaki Nasir Ahmed El-Rufai da Rotimi Amaechi
- Shehu Sani ya bayyana cewa tsofaffin gwamnonin guda biyu ba su da hurumin sukar Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Tsohon sanatan ya zarge su da kitsa matsalar tsaro da yunwa a lokacin da suka riƙe madafun iko a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Sanata Shehu Sani ya ce tsofaffin gwamnoni irinsu Nasir El-Rufa’i da Rotimi Amaechi ba su da hurumin caccakar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shehu Sani ya zarge su da cewa su ne gwanayen da suka assasa matsalar ƴan bindiga da yunwa a Najeriya.

Source: Facebook
Tsohon sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa ta takwas, ya zarge su da munafurci da nuna son kai a siyasa, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu Sani ya nuna yatsa ga Amaechi, El-Rufai
Shehu Sani ya kuma soke su kan yadda suke ɗora laifin hauhawar yunwa da talauci a ƙasar nan kan manufofin Shugaba Tinubu.
Ya ce El-Rufa’i da Amaechi ba su da wani hurumin sukar wannan gwamnati, ganin cewa su ma a lokacin da suke kan mulki ba su magance irin waɗannan matsaloli ba.
“El-Rufa’i da Amaechi ya kamata su sunkuyar da kansu da kunya. Su ne suka assasa matsalolin ƴan bindiga, talauci da yunwa da suke kamar suna kukan su a yanzu."
"A lokacin da suke mulki, ba su ɗauki wani mataki ba don warware waɗannan matsaloli, amma yanzu suna kuka saboda kawai ba su samu wani matsayi a cikin wannan gwamnati ba."
"Babu laifi a sukar gwamnati, amma idan sukar ta samo asali ne daga jin haushin rashin samun muƙami maimakon damuwa da halin da jama’a ke ciki, hakan na da haɗari."
- Shehu Sani
Shehu Sani ya soki shugabannin gwamnatin Buhari
Tsohon sanatan ya kuma yi tsokaci game da wasu tsofaffin jami’an gwamnatin Muhammadu Buhari da ke yunƙurin bata gwamnatin Tinubu bayan sun kasa samun muƙaman ministoci, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar da batun.

Source: Twitter
"Waɗannan mutanen sun riƙe ragamar mulkin ƙasar nan na tsawon shekaru takwas.”
“Sun samu dama, albarkatu da tasiri da za su iya canja Arewacin Najeriya zuwa abin koyi na ci gaba ga sauran sassan ƙasa. Amma maimakon haka, sun bar yankin a cikin wani hali mafi muni."
A yau, mutane za su iya bin hanyar Birnin Gwari, wadda a baya ta zama tarkon mutuwa saboda yawan hare-haren ƴan bindiga."
"Kudancin Kaduna wanda a baya aka watsar da shi, yanzu ya samu zaman lafiya saboda ƙoƙarin babban hafsan hafsoshin ƙasar nan."
- Shehu Sani
Shehu Sani ya ba ƴan Arewa shawara kan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya shawarci ƴan Arewa kan zaɓen shekarar 2027.
Shehu Sani ya buƙaci mutanen Arewacin Najeriya da su marawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya a babban zaɓen 2027 da ake tunkara.
Tsohon sanatan ya nuna cewa ya kamata mutanen Arewa su haƙura da neman shugabanci har sai yankin Kudu ya kammala shekara takwas a kan madafun ikon ƙasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


