Sallah: Sarki Sanusi II Ya Fitar da Sanarwar Shirin Hawa a Kano, Ya Umarci Hakimai
- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ba da umarni ga dukkan hakiman masarautarsa kan shirin hawan sallah da za a gudanar cikin makon nan
- Sanarwar da Damakwayon Kano ya fitar ta bukaci hakimai da su hallara da dawakansu ranar Laraba a cikin birnin Kano kafin babbar sallah
- Majalisar masarauta ta ce za a gudanar da taro a fadarsa don bayyana yadda za a tafiyar da hawan, tare da haɗin gwiwar kananan hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya fitar da sanarwa game da bukukuwan sallah babba da ake shirin yi.
Basaraken ya fitar da sanarwar ana saura kwana uku a gudanar da bikin babbar sallah a ranar Juma'a 6 ga watan Yunin 2025.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da Damakwayon Kano, Alhaji Abba Yusuf, ya fitar ranar Talata, cewar TRT Hausa.

Kara karanta wannan
Eid El Adha: 'Yan sanda sun sake cin karo da Sarki Sanusi II, an haramta hawan Sallah a Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda hawan sallah ke jawo rudani a Kano
Hawan sallah a Kano ya sha jawo ka-ce-na-ce saboda samun hatsaniya da ake yawan yi yayin gudanar da shi.
A karamar sallah da ta wuce, bayan shirya hawa, rundunar yan sanda ta umarci dakatar da shi saboda dalilai da tsaro.
Tun farko, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya shirya hawa kafin daga bisani ya janye saboda maslahar tsaro.
Dalilin yan sanda na gayyatar Sanusi II
Duk da umarnin yan sanda, Sarki Sanusi II ya yi hawa da motoci a birnin Kano wanda daga bisani aka samu hatsaniya har da rasa rai.
Daga bisani, yan sanda sun gayyace shi zuwa Abuja domin amsa tambayoyi game da bijirewa umarninsu kan hawa a Kano.
Wannan umarni na yan sanda ya bar baya da kura inda al'umma ke ganin an ci mutuncin Sarki duba da irin kimar da yake da shi a jihar da kasa baki daya.

Source: Twitter
Wane umarni Sanusi II ya ba hakimai?
Sarki Sanusi II ya umurci dukkan hakimansa da su shirya tsaf domin gudanar da hawan babbar sallah cikin wannan mako mai zuwa, cewar rahoton Leadership.
Sanarwar ta ce:
“Hakimai su zo birnin Kano da dawakansu ranar Laraba 4 ga watan Yunin 2025 da muke ciki.”
Sanarwar ta kuma ce:
“Za a yi taro da Hakimai a fadar Sarki Alhamis domin karɓar umarni da bayani kan hawan.
“An sanar da shugabannin ƙananan hukumomi su taimaka wa hakimai su samu damar halartar hawan babbar sallah cikin birnin Kano.”
Karagar mulki: Sanusi II ya godewa Gwamna Abba
A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana godiyarsa ga Allah da Gwamna Abba Kabir bisa dawowa kujerar sarautar bayan tsige shi.
Sarkin ya soki gwamnatin da ta shude kan kirkirar sababbin masarautu da ya ce ya saba da tarihi da tsarin da iyaye da kakanni suka gada
Basaraken ya roki Allah ya kara hada kan gidansu, ya dawo da zaman lafiya, arziki da damina mai albarka a jihar Kano inda ya yi wa Gwamna Abba Kabir alkawari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
