Bayan Ganawa da Wakilan Gwamnati, Ma'aikatan Shari'a Sun Amince a Janye Yajin Aiki
- Ƙungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya (JUSUN) ta cimma matsaya da wakilan gwamnati, ta dakatar da yajin aikin da take yi
- JUSUN ta yanke wannan shawara ne bayan doguwar tattaunawa da wakilan shugaban alkalan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki
- Sanarwar ta tabbatar da cewa idan gwamnati ta saki kuɗin da ake bukata, za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ƙungiyar ma’aikatan ɓangaren shari’a ta Najeriya, (JUSUN) ta dakatar da yajin aikin da take yi, tare da umurta 'ya'yantata su koma bakin aiki daga ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban ƙasa na ƙungiyar ya fitar tare da sanya hannu da wasu shugabannin ƙungiyar 10.

Source: Getty Images
Channels TV ta wallafa cewa shugabannin sun bayyana cewa sun yanke hukuncin dakatar da yajin aikin ne bayan dogon nazari kan batutuwan da suka shafi abin da jawo yajin aikin tun farko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A taron da aka yi, sun haɗa da tattaunawa da wakilan shugaban alkalan Najeriya, Justice Kudirat Kekere-Ekun, da kuma sauran manyan masu ruwa da tsaki a harkar shari’a, a ranar Talata.
Kungiyar JUSUN ta amince da janye yajin aiki
Leadership News ta kara da cewa JUSUN ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne bayan amincewa da roƙon shugaban alkalan ƙasa (CJN), da ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Muhammad Dingyadi.
Sai kuma jagororin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC), da wasu sauran masu ruwa da tsaki da suka saka baki a cikin lamarin domin kawo daidaito.
Daya daga cikin abubuwan da aka cimma a yarjejeniyar shi ne cewa dakatar da yajin aikin zai ba wa JUSUN damar ci gaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya domin a saki kuɗinsu a wata daya.

Source: Twitter
A cikin sanarwar da aka fitar, an bayyana cewa:
“Da zarar an saki kuɗin da ya kamata a bai wa bangaren shari’a, za a aiwatar da bukatun JUSUN na sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da kuma bashin da ya taru, za a biya ƙarin albashi na 25% da 35%, da kuma kyautar albashi na watanni 5 da dukkan kuɗin baya da suka taru.”
JUSUN: Masu ruwa da tsaki a hana yajin aiki
Baya ga mataimakin shugaban ƙasa na JUSUN, sauran da suka rattaba hannu sun haɗa da: Sakataren kuɗi na ƙasa (na biyu), kotun daukaka ƙara,da babbar kotun tarayya.
Sai kuma kotun masana’antu, babbar kotun Abuja, kotun Musulunci da Kotun Al’ada na Abuja, hukumar gudanar da shari’a ta FCTda sauransu
Ma'aikata sun fara yajin aiki a kotu
A baya, mun wallafa cewa ma'aikatan shari'a a Najeriya karkashin kungiyar JUSUN sun fara yajin aiki na kasa, wanda ya haifar da rufe kotuna a fadin kasar.
A Ibadan, jihar Oyo, an hana alkalai, lauyoyi da sauran jami'an shari'a shiga kotuna, ciki har da babbar kotun tarayya, kotun daukaka kara da kotun kwadago ta kasa.
Yajin aikin ya samo asali ne daga bukatar ma'aikatan shari'a na karin albashi na 25% da 35%, da kuma biyansu alawus da sauran hakkokinsu da suke bin gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


