Abba Ya Shiga Madafin 'Yan Kano a Saudiyya don Duba Abincin da ake Rabawa
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar bazata domin duba yadda ake dafa abinci ga mahajjatan Kano a Saudiyya
- Ya yaba da tsafta da ingancin girki, inda ya jaddada cewa lafiyar mahajjatan na da nasaba da nau’in abincin da suke ci
- Ziyarar ta gudana ne da nufin tabbatar da kyakkyawan shiri yayin da mahajjatan ke shirin tafiya Mina domin ci gaba da ibada
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - A shirye-shiryen da mahajjatan Kano ke yi na tafiya Mina, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai wata ziyarar bazata babban dakin girki da ke kula da abincin mahajjatan jihar.
Ziyarar ta gudana ne a daren Lahadi, inda gwamnan ya duba inganci, tsafta da kuma yanayin hadin gwiwar da ake yi wajen raba abinci ga mahajjata da ke karkashin NAHCON.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da hadimin gwamnan, Ibrahim Adam ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya zagaya sassan girkin gaba ɗaya, ciki har da inda ake dafa abinci, ajiya, da kuma duba irin kayan lambu da ake amfani da su, ya ce lafiya da jin daɗin mahajjata na da muhimmanci.
Abba ya duba tuwo da miyar kuka a Saudiyya
Yayin ziyarar, an dafa tuwo da miyar kuka mai haɗe da naman shanu, abincin gargajiya na Hausawa da aka saba da shi Arewa.
Gwamna Abba ya ɗibi abincin da kansa domin tabbatar da ingancin girkin da kuma yadda ya dace da ka’idojin abinci mai lafiya.
Ya kuma duba kayan ciye-ciye da ‘ya’yan itatuwa da ake baiwa mahajjatan kamar tuffa, lemu da ruwan kwalba.

Source: Facebook
Abba Kabir ya yi haka ne don tabbatar da cewa mahajjatan na samun isasshen ruwa da abinci mai kyau a yanayin zafin Saudiyya.
Gwamnan ya yaba da aikin kamfanin girki na Na’ima Idris Kitchen da ke da alhakin kula da abincin mahajjatan Kano.
Abba Kabir Yusuf ya gargade su da kada su yi sakaci ko gajiyawa, yana mai cewa nauyin da ke kansu na da girma.
Abba ya nemi a cigaba da kokari a Saudiyya
Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga ma'aikata masu girkin da su cigaba da kokari wajen yin gaskiya da amana.
A cewar gwamnan:
“Aiki ne na amana. Muna sa ran za ku ci gaba da ƙoƙari. Ba za mu lamunci sakaci ba, musamman a wannan muhimmin lokaci na hajji,”
Shugaban kamfanin girkin ya gode wa gwamnan bisa ziyarar da ya kai tare da tabbatar masa da cewa za su cigaba da gudanar da aiki cikin ƙwarewa da biyayya ga umarni.
Shugaba kamfanin ya ce:
“Ziyararku ta ƙara mana ƙwarin gwiwa. Za mu tabbatar mun ci gaba da yin aiki yadda ya dace,”
An kama 'yan Kano suna shirin zuwa Saudiyya
A wani rahoton, kun ji cewa an kama wasu mutane biyu a jihar Kano suna kokarin tafiya kasar Saudiyya.
Rahoto ya nuna cewa bayan bincike mai zurfi an gano cewa wasu mutane ne suka dauki nauyin mutanen domin tafiya Saudiyya da kwaya.
Legit ta rahoto cewa jami'an hukumar NDLEA sun kama wasu mutane da ake zargi suna cikin masu daukar nayin mutanen zuwa Saudiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


