Faransa ta Lissafa Kungiyoyi 19 da Ta Rabawa Kudin Tallafi N1.8bn a Najeriya
- Ofishin jakadancin Faransa a Najeriya ya bayyana sunayen kungiyoyin da suka ci gajiyar tallafin €1m domin ci gaban al’umma
- An zabi kungiyoyi 19 daga jihohi 14 da Babban Birnin Tarayya Abuja don aiwatar da ayyukan raya kasa a matakai daban daban
- Shirin tallafin ya mayar da hankali ne kan yaki da rashin daidaito, ƙarfafa mata da kuma karfafa gwiwar al’umma a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ofishin jakadancin kasar Faransa a Najeriya ya fitar da sunayen kungiyoyin fararen hula da suka ci gajiyar tallafin €1m (kimanin Naira biliyan 1.8) domin gudanar da ayyuka.
Legit ta rahoto cewa a makon da ya wuce ne aka yi wani taro a Abuja domin raba wa kungiyoyin tallafin kudin.

Source: Twitter
A cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), an zabi kungiyoyi 19 daga jihohi 14 da Babban Birnin Tarayya, domin gudanar da ayyukan da za su amfani al’umma kai tsaye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tallafin, wanda aka fi sani da French Embassy Fund for Civil Society Organisation (FEF-OSC), ya cikin shekara ta shida da ake gudanar da shi domin karfafa kungiyoyin fararen hula a Najeriya.
Kungiyoyin da suka samu tallafin Faransa
Daga cikin kungiyoyin da aka bayyana sunayensu akwai Against All Odds Foundation da Grassroot Researchers Association daga jihar Adamawa.
Baya ga haka akwai Girl Child Values Support Initiative da Youth and Adolescent Health Initiative and Counselling daga jihar Bauchi.
Haka kuma akwai RACE Africa daga Benue; Economic and Social Empowerment of Rural Communities daga Enugu.
Rahoton Premium Times ya nuna cewa akwai Empower to Thrive Development Initiative daga Babban Birnin Tarayya Abuja.
Karin kungiyoyin Najeriya da Faransa ta tallafawa
A jihar Imo akwai Circuit Pointe; a Kaduna Anti-Sexual Violence Lead Support Initiative; a Kano Bridge Connect Africa Initiative; sannan a Kogi akwai Protect the Child Foundation.

Kara karanta wannan
Tun ba ayi zaben 2027 ba, an fadi yankin da ya kamata shugaban kasa ya fito a 2031
Sauran sun hada da Hopesalive Initiative for Africa-HAI da Humanity Family Foundation for Peace and Development daga jihar Legas; da Olive Rights to Health Initiative daga Nasarawa.
A jihar Neja kuwa akwai Community Health Initiative for Youth in Nigeria da RippleAfrica Trust Foundation; a Oyo kuwa akwai Committed Soul Women Health Advocacy Africa Initiative.
A jihar Zamfara, an bayyana Gender Equality, Peace and Development Centre da Protection Without Borders League a matsayin wadanda suka samu kudin.
Aikin da za a yi da tallafin Faransa a Najeriya
Jami'in Faransa a Najeriya, Bertrand de Seissan ya bayyana cewa shirin zai bayar da taimakon kudi da na fasaha ga kungiyoyin domin magance manyan kalubale.

Source: Twitter
Ya bayyana cewa shirin na wannan shekarar ya mayar da hankali ne kan matsalolin da suka hada da rashin daidaito tsakanin jinsi, talauci da kuma karfafa gwiwar jama'a.
Faransa za ta tallafawa jami'an Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Faransa ta fara cika wasu alkawura da ta cimma da shugaban Najeriya, Bola Tinubu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Faransa za ta horas da jami'an hukumar NDLEA a Najeriya domin kara samun kwarewa.
Hukumar NDLEA ta yi karin haske kan matakin da kasar Faransa ta dauka tare da mika godiya ga shugabannin kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

