Hajjin Bana: Wata Mahajjaciya daga Najeriya Ta Sake Rasuwa a Asibitin Makkah
- Majiyoyi sun tabbatar da rasuwar wata mahajjaciya daga jihar Plateau da ta je aikin hajji a kasar Saudiyya a ranar Litinin
- Sakataren hukumar jin daɗin alhazai, Daiyabu Dauda, ya ce an kai mamaciyar asibiti bisa umarnin Gwamna Caleb Mutfwang
- An yi jana’izarta a babban masallacin Makka, jami’ai da ’yan uwa sun halarta kuma an kuma birne ta bisa tsarin addinin Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makkah, Saudiyya - An shiga wani irin yanayi bayan sanar da rasuwar wata mahajjaciya daga jihar Plateau a birnin Makkah da ke Saudiyya.
Majiyoyi sun tabbatar da rasuwar Hajiya Jamila Muhammad daga jihar Plateau a ranar Litinin 2 ga watan Yunin 2025.

Source: Original
Hadimar Gwamna Caleb Mutfwang a bangaren yada labarai, Aisha Muhammad ita tabbatar da haka a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hajji: Yawan wadanda suka rasu a Saudiyya
Rahotanni sun ce ana zaton wannan rashi shi ne na shida da aka yi na yan Najeriya da ke aikin hajji a Saudiyya.
An tabbatar cewa bayan rashin yar jihar Edo, akwai wani daga Sokoto da kuma mata daga jihar Benue da wasu a Abia da Imo sannan wannan rashi na Plateau.
Ana yawan samun rasuwar mahajjata a Saudiyya sanadin rashin lafiya da kuma tsananin zafi da aka samu musamman a bara.
Dattijuwa daga Edo ta rasu a Saudiyya
A makon da ya gabata wata Hajiya daga jihar Edo ta rasa ranta a asibitin birnin Makkah bayan fama da rashin lafiya.
An tabbatar da mutuwar mata mai shekaru 75 daga Jihar Edo, Adizatu Dazumi a Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin bana.
An ce Dazumi ta kamu da rashin lafiya bayan kammala dawafi a Ka’aba, sannan aka garzaya da ita asibitin Sarki Fahad da ke birnin Makkah.

Source: Facebook
Wata mahajjaciyar Plateau ta rasu a Saudiyya
Hadimar gwamnan Plateau, Aisha ta ce marigayiyar ta rasu a birnin Makka a Saudiyya a jiya Litinin sakamakon ciwon suga.
Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren hukumar Alhazan jihar Plateau, Alhaji Daiyabu Dauda ya fitar game da rashin da aka yi.
A cewar Alhaji Daiyabu Dauda, likitoci sun tabbatar da rasuwarta a Asibitin Sarki Abdul’aziz bayan ta sha fama da jinya.
Da aka sanar da shi batun, Daiyabu ya umurci likitoci su gaggauta kai ta asibiti domin samun kulawar da ta dace bisa umarnin Gwamna Caleb Mutfwang.
Ya bayyana cewa Amirul Hajj da wasu jami’ai da ’yan uwa sun halarci sallar jana’iza a babban masallacin Makka, inda aka birne ta.
Jami'in ya mika sakon ta’aziyya ga Gwamnatin Plateau, ’yan uwa da abokan arziki, yana addu’ar Allah ya gafarta mata, ya saka ta cikin Aljannatul Firdaus.
Mahajjaciya 'yar Plateau ta tsinci N8m a Saudiyya

Kara karanta wannan
Hajjin bana: Za a fassara hudubar Arfah zuwa Hausa, Fulatanci da sauran harsuna 32
Kun ji cewa ƴar Najeriya daga cikin mahajjatan bana, Hajiya Zainab ta mayar da $5,000 da ta tsinta ga mai su dan ƙasar Rasha.
Hajiya Zainab ta tsinci kuɗin, da suka kai kimanin ₦8m a masallacin Harami da ke Makkah, amma ba ta yi wata-wata ba ta maida wa mai su.
Hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) da hukumar jin daɗin alhazan jihar Plateau sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka yabawa matar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

