Tsautsayi: Yadda Wani Mahaifi Ya Dirkawa Dansa Bindiga har Lahira

Tsautsayi: Yadda Wani Mahaifi Ya Dirkawa Dansa Bindiga har Lahira

  • Wani mahaifi ya shiga matsanancin hali bayan ya harbi ɗansa mai shekaru 15 har lahira bisa kuskure suna tsaka da aikin gona
  • Rundunar yan sandan jihar Ekiti ta tabbatar da cewa mutumin ya dauki dansa ya taya shi aiki a gona a lokacin da lamarin ya faru
  • Binciken farko ya bayyana cewa mutum na fama da matsalar birrai dake masa ta'adi a gonar, kuma sai ya ji motsi a saman bishiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ekiti –Wani yaro mai shekaru 15 ya rasa ransa a cikin wani mummunan lamari da ya faru a ƙauyen Iye Ekiti da ke Ƙaramar Hukumar Ilejemeje a Jihar Ekiti.

Mahaifinsa ne ya dirkawa dansa bindiga bisa kuskure, inda ya bayyana cewaya dauka yaron biri ne.

Kara karanta wannan

'Duk mun koma mayunwata': Tsohon minista ya fadi abin da ke jiran Tinubu a 2027

Ekiti
Wani mahaifi ya kashe dansa a Ekiti Hoto: Legit.ng
Source: Facebook

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a gonar magidancin yayin da yake aiki tare da ɗansa ganin damuna ta fara sauka duk da cewa bai ga ya bar kusa da shi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa baki daya al'amarin ya faru bisa kuskure, domin bai san cewa dansa ne wanda ya yi motsin da ya jawo ya yi harbi ba.

'Yan sanda sun tabbatar da kisan yaron

Kwamishinan ’yan Sanda na Jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya tabbatar da faruwar al’amarin a ranar Litinin, 2 ga watan Yuni, 2025 bayan an fara kwarya kwaryar bincike.

Ya tabbatar da cewa manomin ya saba fuskantar hare-haren birrai a gonarsa, don haka ya ɗauki bindiga domin kare amfanin da ke gonar.

Bincike na farko da ’yan sanda suka gudanar ya nuna cewa mutumin ya hango motsi a wata bishiya kusa da inda yake, sai ya harba bindigar, yana tunanin biri ne.

Kara karanta wannan

Magidanci ya kidime, ya suma bayan matarsa ta haifi 'yan 3 a asibitin Kogi

Yan sanda
Yan sanda sun fara binciken kisan yaro a Ekiti Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Amma abin takaici, daga bisani sai ya gano cewa ɗansa ne ke kan bishiyar, wanda ya rigamu gidan gaskiya sakamakon harbin ba tare da bata lokaci ba.

Rundunar yan sandan ta tabbatar da cewa an tsare mutumin domin ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, yayin ci gaba da gudanar da tambayoyi kan yadda abin ya faru.

Rundunar ta tabbatar da cewa ana samun hadin kai domin a samo bayanai, gabanin a dauki mataki na gaba a kan mummunan al'amarin da ya gigita jama'a.

Wani ya kashe dansa a Bayelsa

A baya, mun wallafa cewa wani lamari mai tayar da hankali ya auku a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa, inda wani mutum mai suna Vwede ya lakadawa ɗansa mai shekaru biyu duka.

Lamarin ya jawo babbar matsala musamman bayan karamin yaron ya mutu sakamakon bugun da ya sha, a ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba, 2021 a titin Imiringi da ke Yenagoa na Bayelsa.

Shaidu sun ce Vwede, wanda ya fito daga Jihar Delta, ya yi wa yaron nasa bulala mai tsanani, inda daga bisani yaron ya suma, inda mahaifin ya ɗauke shi zuwa wani asibiti da ke kusa da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng