Wani mahaifi ya kashe dansa mai shekaru 2 da tsananin duka da bulala

Wani mahaifi ya kashe dansa mai shekaru 2 da tsananin duka da bulala

  • Wani mahaifi ya tsere bayan da ya hallaka dansa na cikinsa har lahira kuma ya kaishi asibiti
  • Rahoto ya bayyana cewa, mutumin ya zane yaron da bulala ne lamarin da ya kai ga mutuwarsa
  • A halin da ake ciki 'yan sanda da masu rajin kare hakkin dan Adam sun shiga lamarin don gano mutumin

Bayelsa - Wani mutum mai suna Vwede ya lakadawa dansa mai shekaru biyu duka har lahira a Yenagoa, jihar Bayelsa kuma ya tsere, The Nation ta ruwaito.

Lamarin, wanda ya faru ranar Lahadi 26 ga watan Satumba a kan titin Imiringi a Yenagoa, ya jawo Allah wadai daga makwabta da masu rajin kare hakkin dan adam.

An tattaro cewa mahaifin da ake zargi, daga jihar Delta, ya yi wa yaron mai shekaru biyu bulala mai tsanani sannan ya kai shi asibiti a kan hanyar Ruthmore Hotel a Immiringi bayan yaron ya suma.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Wani mahaifi ya kashe dansa mai shekaru 2 da tsananin duka da bulala
Taswirar jihar Bayelsa | Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Sai dai ya tsere bayan ma'aikatan lafiya da ke bakin aiki sun tabbatar masa da cewa yaron da ya kawo asibitin ya mutu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma tattaro cewa watakila mahaifiyar yaron ta yi watsi da yaron tare da mahaifinsa ne kuma ta gudu bayan ta haihu.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin akwai sarkakiya a cikinsa kasancewar mahaifin ya tsere kuma ba a san inda yake ba a halin yanzu.

Ya ce ba a san ko wanene mutumin ba kuma tun daga lokacin ya tsere, don haka ya dagula yanayin bincike, inji rahoton Daily Trust.

Tuni, lauyoyi mata da wadanda ke da hannu a yakin da ake yi da cin zarafin jinsi a jihar Bayelsa sun nuna fushinsu kan lamarin.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Shugaban Gidauniyar Doka ta Do, Barr Stanley Churchill Aimiekumo, ya ce maigidan da mahaifin ke zaune ya kira gidauniyar don sanar da su game da barnar, inda ya yi ikirarin cewa mahaifin yana azabtar da yaron dan shekara biyu kafin ma ya hallaka shi.

Kodinetan Jiha na gidauniyar Do, Barr. Comfort Itoru, ya ce an kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Akenfa kuma mahaifin ya tsere.

Rami ya rufta da masu hakar ma'adanai, 3 sun mutu, da dama sun jikkata

A wani labarin, Mutane uku sun mutu bayan da wata mahakar ma'adanai da suke aiki a ciki ta rufta a yankin Anyiin da ke karamar hukumar Logo a jihar Benue, ranar Talata 28 ga watan Satumba.

Wakilin Daily Trust ya tattaro cewa marigayan sun kasance suna cikin hako ne lokacin da ramin ya rufta dasu.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce mamatan sun mutu nan take yayin da mutanen gari kuwa suka yi kokarin ceto wadanda suka jikkata.

Kara karanta wannan

Rami ya rufta da masu hakar ma'adanai, 3 sun mutu, da dama sun jikkata

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.