Yaran Talakawan Kano a Makarantu 3,000 za su Amfana da Kudin Jarrabawa Kyauta

Yaran Talakawan Kano a Makarantu 3,000 za su Amfana da Kudin Jarrabawa Kyauta

  • Gwamnatin Kano ta dauki nauyin kudin jarrabawar NECO da NBAIS na dalibai 3,526 daga makarantun sa kai da na al’umma a jihar
  • Hukumar dake kula da ilimi ta Kano (KERD) ta umarci daliban da su garzaya makarantunsu domin daukar bayanan fara yi masu rajista
  • Mutane da dama sun nuna farin ciki da wannan ci gaba tare da yin addu’ar samun nasarar Gwamna Abba a wa’adi na biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da biyan kudin rajistar jarrabawa ga dalibai 3,526 da ke makarantun al’umma da na sa kai a jihar.

Daliban za su yi jarrabawar kammala Sakandare ta NECO da ta Hukumar Nazarin Harshe da Ilimin Addinin Musulunci (NBAIS) na bana ba tare da biyan ko kwabo ba.

Kara karanta wannan

Karatu kyauta: Gwamnatin Tinubu za ta fara ba 'yan makarantun fasaha kudi a wata

Gwamna
Gwamnatin Kano za ta sake biyawa dalibai kudin jarrabawar gama sakandare Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai baiwa gwamna shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Ibrahim Adam, ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin gwamnatin Kano na biyan kudin jarrabawa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna ya yanke shawarar daukar nauyin rajistar jarrabawar ne bayan daliban sun ci jarrabawar cancantar a biya masu kudin da ake kira 'qualifying.'

Gwamna
Gwamnatin Kano za ta biya kudin jarrabawar NECO da NBAIS Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A cewarsa, Hukumar Kula da Ilimi ta Jihar Kano (KERD) ta bukaci daliban da su garzaya makarantunsu domin daukar bayanansu da sauran abubuwan da suka dace.

A baya-bayan nan ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya biya kudin NECO na dalibai 111,316 daga makarantun gwamnati da ke fadin jihar Kano.

Jama’a sun godewa gwamnatin jihar Kano

Wasu daga cikin masu bibiyar Ibrahim Adam a shafin Facebook sun bayyana farin cikinsu da yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ke baiwa ilimi muhimmanci a Kano.

Kara karanta wannan

Ana kiki kaka kan zarginsa da cin zarafi, Akpabio ya goyi bayan karo mata a majalisa

Da dama daga cikinsu sun bayyana fatan ganin gwamnatin sa ta sake dawowa wa’adi na biyu domin ci gaba da aiwatar da ayyukan raya jihar.

Musbahu Galadima Kabo ya ce:

"Hudu a tara da hudu."

Mukidad Uba Abdullahi ya ce:

"To ko makarantar nan za mu koma ne? Naga garabasar tana neman yawa fa oga."

Bello Bubagama ya yi addu’a:

"Allah Madaukaki ya ci gaba da shiryar da kai, ya kare ka, ya albarkace ka da yawa. Muna godiya matuka da duk abin da kake yi mana a jihar nan."

Hon. Sani Dambu Dorayi ya ce:

"Masha Allah. Me girma gwamna, komai yana tafiya yadda ake so."
Akwai makarantar firamare dake filin tsamiya Yara suna karatu a kasa duba da ajin langa langa wasu suke shiga suke karatu a ciki. Akwai fili a jikin makaranta wanda idan ya zama mallakin makaranta shi ne zai sa a samu karin ajujuwa da yara suke karatu yanzu haka a soron gidajen mutane ake karatu ga damuna. Allah yasa me girma gwamna Ya duba koken mu.

Gwamnatin Kano ta biya kudin NECO

Kara karanta wannan

Gwamnoni 36 sun nuna damuwa bayan ambaliya ta ruguza gidaje da mutane a Neja

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta ware sama da Naira biliyan uku domin biyan kudin jarrabawar NECO, NABTEB da NBAIS ga dalibai 141,175.

A cewar Kwamishinan Ilimi na jihar, Ali Haruna Makoda, daliban da suka ci darussa biyar a jarrabawar tantance wadanda za su cancanci tallafin ne suka ci moriyar shirin.

Sanarwar ta bayyana cewa tun daga lokacin da Gwamna Abba ya hau mulki, gwamnatinsa ta biya kudin jarrabawar WAEC, NECO, NABTEB da NBAIS ga daliban da ba su da karfi a Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng