"Shugabanci Akwai Wahala," Gwamna Ya Roki Malamai Su Riƙa Gaya Masu Gaskiya

"Shugabanci Akwai Wahala," Gwamna Ya Roki Malamai Su Riƙa Gaya Masu Gaskiya

  • Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya ce shugabanci amana ce ba kofin gasa ba, yana mai cewa zai ci gaba da kokarin sauke nauyin al'umma
  • Dikko Raɗɗa ya ce jagoranci abu ne mai matuƙar wahala kuma ya zama dole shugabanni su jure suka da cin mutunci daga wasu ƴan ƙasa
  • Gwamnan ya faɗi haka a wurin taron addu'a na musamman da gwamnatinsa ta shirya domin bikin cika shekara biyu a mulki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa shugabanci aiki ne mai matuƙar wahala.

Gwamna Radda ya ja hankalin shugabanni da cewa ya zama dole su jure suka da kalaman cin mutunci daga wasu ‘yan ƙasa.

Gwamna Dikko Radda.
Gwamnan Katsina ya ce shugabanci na da matuƙar wahala Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Katsina ranar Alhamis, a wani taron addu’a na musamman da gwamnatinsa ta shirya domin cika shekaru biyu a kan mulki.

Kara karanta wannan

Musulmi sun yi babban rashi, Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Sakataren watsa labaran gwamnan Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammaed ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a Facebook.

Gwamna Dikko ya koka kan wahalar jagoranci

A jawabinsa, Gwamna Radda ya yi karin haske kan kalubalen da ke tattare da jagoranci, yana mai ba da tabbacin cewa zai ci gaba da kamanta gaskiya da rikon amana wajen gudanar da aikinsa.

“Duk da mun san akwai masu sukarmu amma na san masu yaba ayyukan gwamnatinmu da jajircewarmu sun fi yawa,” in ji shi.

Dikko Ya ƙara da cewa, shugaba mutum ne kamar kowa, kuma ba zai rasa kuskure ba, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne ayyukan alherinsa su fi yawa.

“Ku sani, dukiya da gwamnati ke gudanarwa ta talakawa ce, mu da muke ofis muna kula ne da dukiyarku,” in ji shi.

Rayuwar Dikko Radda ta sauya bayan hawa mulki

Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa rayuwarsa ta sauya gaba ɗaya tun da ya hau mulki, domin a yanzu ba ya samun damar yin abin da yake so.

Kara karanta wannan

"Lokaci ya yi da zan bar PDP," Gwamna ya ƙara nuna alamun zai koma APC kafin 2027

"Yanzu na zama kamar wanda aka kulle. Wani lokaci ba na iya gudanar da rayuwata kamar yadda nake so, domin idan na fita daga gida da safe sai dare zan koma."
“Wannan aiki yana buƙatar sadaukarwa da jajircewa. Ina godiya da yadda mutane ke tarbar mu a ko ina da farin ciki, hakan na ƙarfafa gwiwarmu wajen yin abin da ya dace.”
"Idan mutane suna yaba maka, suna fadin alheri a kanka, amma kuma ka ci amanarsu, to ba makawa Allah zai hukunta ka."

- Malam Dikko Radda.

Dikko Radda.
Gwamna Dikko Radda ya bukaci malamai su rika kai masu koken talakawa Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamna ya roƙi malamai su faɗa masu gaskiya

Gwamnan ya jaddada cewa ko wanne lokaci kofarsa a buɗe take don karɓar shawara da gyara, yana mai roƙon malamai da su rika gaya masu yadda al’umma ke ji da yadda abubuwa ke gudana.

Haka kuma, ya bukaci su tallafa wa gwamnati wajen yaki da matsalar tsaro a matakin ƙauyuka, musamman wajen bankado masu ba ‘yan ta’adda bayani da masu fataucin miyagun ƙwayoyi.

Wasu daga cikin mazauna Katsina sun bayyana gwamnatin Dikko a shekara biyu a matsayin ba yabo ba fallasa.

Ahmad Tukur daga ƙaramar hukumar Ɗanja ya shaida wa Legit Hausa cewa Gwamna Dikko ya yi ƙoƙari matuƙa a ɓangaren tsaro domin an samu sauki sosai.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi karatun ta natsu, ya fadi abin da zai hana magance 'yan bindiga

"To ba yabo ba fallasa, ni dai ta wuri ɗaya zan yabi Dikko shi ne tsaro. A zahirin gaskiya ya yi koƙari, ba zan ce an samu tsaro ba amma an samu sauƙi sosai fiye da yadda ya tarar," in ji shi.

Wani matashin ɗan siysa, Kabir A. Kabir ya ce babban matsalarsa da Dikko shi ne yadda ya ki taimakon matasa ta yadda za su gina kansu.

Abin da ke rura wutar matsalar tsaro a Katsina

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Dikko Raɗɗa ya ce sama da kaso 70% na masu rura wutar matsalar tsaro a jihar Katsina ba a cikin daji suke rayuwa ba.

Gwamna Radda ya bayyana cewa suna cikin al'umma suna aiki a matsayin masu bayar da bayanai ga ƴan bindiga, waɗanda aka fi sani da imfoma.

Dikko Raɗɗa ya ce dole sai an magance masu ba ƴan bindiga bayanai kafin a shawo kan matsalar rashin tsaro gaba ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262