Dakarun Sojoji Sun Hallaka Babban Kwamandan Boko Haram da Mayaka Masu Yawa

Dakarun Sojoji Sun Hallaka Babban Kwamandan Boko Haram da Mayaka Masu Yawa

  • Dakarun sojojin Najeriya sun ƙaddamar da wani hari na musamman kan maɓoyar ƴan ta'adda a jihar Borno
  • A harin da sojojin suka kai, sun samu nasarar kashe babban kwamandan Boko Haram da aka daɗe ana nema ruwa a jallo
  • Jami'an tsaron sun kuma kashe mataimakinsa tare da ƙwato makamai masu yawa a artabun da suka yi da ƴan ta'addan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojoji na musamman na rundunar Operation Hadin Kai sun kashe wani shahararren kwamandan Boko Haram/ISWAP, Amir Abu Fatima, a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun hallaka babban kwamandan na Boko Haram ne a wani harin da aka kai kan sansanin ƴan ta’adda a yankin Kukawa na jihar Borno.

Sojoji sun hallaka kwamandan Boko Haram
Dakarun sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta sanya a shafinta na X a ranar Juma'a, 30 ga watan Mayun 2025.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi luguden wuta ta sama da kasa kan Boko Haram, an kashe mayaka 60

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram

An ƙaddamar da harin ne a ranar Alhamis, bayan samun ingantaccen bayanin sirri da ya bayyana inda wannan babban mai laifi ke ɓuya.

Sanarwar ta bayyana cewa Abu Fatima, wanda aka saka tukuicin Naira miliyan 100 a kansa, ya samu mummunan rauni a musayar wuta da sojoji.

Hakazalika an kashe mataimakinsa, wasu ƙwararru kan haɗa abubuwan fashewa, da kuma mayaƙa masu tarin yawa.

“A cikin nasarar yaƙi da ta’addanci, sojojin musamman na Operation Hadin Kai sun kai hari a ranar 30 ga Mayu, 2025, inda suka farmaki muhimmin sansanin Boko Haram/ISWAP a yankin Kukawa na Arewa maso Gabashin jihar Borno."
"Harin da aka gudanar bisa ingantaccen bayanan sirri, an kai sa ne da niyyar farmakar Amir Abu Fatima, wani shahararren kwamandan ƴan ta'adda da aka sanya tukuicin N100m a kansa."
"A yayin musayar wuta mai tsanani, Abu Fatima ya samu mummunan rauni. An kuma kashe mataimakinsa, wasu ƙwararrun masu haɗa abubuwan fashewa da kuma da dama daga cikin mayaƙansa."

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda sama da 30 aka damke suna sayar da makamai ga yan ta'adda

- Rundunar sojojin Najeriya

Sojoji sun ƙwato makamai a hannun ƴan ta'adda

Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai daga wajen ƴan ta'addan a yayin artabun.

Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram
Sojoji sun farmaki 'yan Boko Haram a Borno Hoto: Legit.ng
Source: Original
"Sojojin sun kuma ƙwato bindigogin AK-47 masu yawa, gidajen harsasai, kayan haɗa bam da wasu makamai daban-daban. An kammala aikin ba tare da samun rauni ko asarar rai daga ɓangaren sojoji ba."
"Wannan aiki ya zama babban rauni ga jagorancin ƴan ta’adda a yankin, kuma ya kara tabbatar da ƙudirin sojojin Najeriya na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas."

- Rundunar sojojin Najeriya

Jami'an tsaro sun kashe ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro na DSS da sojoji sun yi aikin haɗin gwiwa don fatattakar ƴan bindiga a jihar Neja.

Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga masu yawa yayin wani artabu da suka yi a ƙaramar hukumar Munya.

An samu nasarar ne bayan da ƴan bindigan suka kai hare-hare kan wasu ƙauyuka da ke ƙaramar hukumar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng