INEC Ta Sanar da Ranakun da za a Yi Zaben Gwamnoni a Osun da Ekiti a 2026
- Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta bayyana ranakun da za a gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Ekiti da Osun a shekarar 2026
- Zaɓen gwamna a jihar Ekiti zai gudana ranar Asabar, 20 ga Yuli, 2026, yayin da na Osun zai gudana ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026
- Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yaku ya bayyana hakan ne yayin rantsar da sababbin kwamishinonin zaɓe guda shida a Abuja
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana jadawalin zaɓukan gwamna da za a gudanar a jihohin Ekiti da Osun.
Hukumar INEC ta bayyana cewa zaɓuka biyun za su gudana a watan Yuli da Agusta na shekarar 2026.

Source: Facebook
Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da haka wajen bikin rantsar da sababbin kwamishinonin zaɓe guda shida a Abuja kamar yadda INEC ta wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika ya ce INEC ta kammala shirin gudanar da zaɓukan cike gurbi a majalisun dokokin ƙasa da na jihohi domin maye guraben da aka samu.
Ranakun zaben Ekiti da Osun a 2026
Hukumar INEC ta bayyana cewa zaɓen gwamna a jihar Ekiti zai gudana ranar Asabar, 20 ga Yuli, 2026.
Sai kuma zaɓen gwamnan jihar Osun zai gudana a ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026, kamar yadda doka ta tanada.
A cewar Farfesa Mahmood Yakubu, jam’iyyun siyasa za su fara gudanar da zaɓen fidda gwani a Ekiti daga 20 ga Oktoba zuwa 10 ga Nuwamba, 2025.
Daga nan ne za su tura sunayen ‘yan takara zuwa shafin yanar gizo na INEC kafin 22 ga Disamba, 2025.
A Osun kuwa, za a fara zaɓen fidda gwanin daga 24 ga Nuwamba zuwa 15 ga Disamba, 2025, sannan a rufe shafin tura sunaye zuwa 9 ga Fabrairu, 2026.
An saka jadawalin zaɓen a shafin INEC
Farfesa Yakubu ya ce an saka cikakken jadawalin zaɓen da ayyukan da ke tattare da shi a shafin yanar gizo da shafukan sada zumunta na INEC domin sauƙaƙa fahimta ga ‘yan siyasa da al’umma.
Ya kuma tabbatar da cewa INEC za ta fara aikin rijistar masu kaɗa ƙuri’a nan ba da jimawa ba, musamman ganin cewa zaɓen gwamna na jihar Anambra na karatowa.
An rantsar da kwamishinonin INEC 6
A yayin bikin, Farfesa Yakubu ya ce rantsar da sababbin kwamishinonin zaɓe guda shida ya cike gibin da ake da shi a cikin jihohin Najeriya da babban birnin tarayya.
The Nation ta wallafa cewa ya ja kunnensu kan cewa gudanar da zaɓe ba aiki ba ne kawai da za a yi yadda aka gadama, sai dai amana ne da ke bukatar bin ƙa’idojin zabe.

Source: UGC
INEC za ta kawo sauye sauye a zabuka
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban hukumar INEC ya sanar da cewa suna son yin sauye sauye kafin zaben 2027.
Farfesa Mahmood Yakubu ya ce daga cikin sauye sauyen da suke so shi ne wanda zai ba mutum damar kada kuri'a ba tare da katin PVC ba.
Shugaban INEC ya ce hakan zai taimaka wajen rage kudin da gwamnati ke kashewa wajen samar da katin PVC a duk lokacin zabe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

