Tashin Hankali: 'Yan Daba Sun Farmaki Kamfanin Siminti a Gombe, An Kashe Mutum 1
- Wasu 'yan daba dauke da makamai sun kai hari tashar jirgin sama na kamfanin Ashaka da ke Gombe, inda suka yi yunkurin sace kayan aiki
- Sun fara kai farmaki kan jami'an tsaro, sannan suka nufi katangar jirgin saman don lalata ta tare da kokarin kwashe kayayyakin da ke ciki
- Sai dai jami'an NSCDC sun dakile su, inda suka harbi ɗaya aga cikinsu, wanda ya mutu daga baya yayin da ragowar suka ranta a na kare
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gombe - Wasu 'yan daba da ba a san ko su waye ba sun kai farmaki a kamfanin siminti na Ashaka da ke Bajoga, karamar hukumar Funakaye a jihar Gombe.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 11:43 na daren ranar Alhamis, 29 ga Mayu, 2025, kuma ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaya daga cikin masu harin.

Source: Getty Images
'Yan daba sun farmaki kamfanin simintin Ashaka
Kamar yadda masanin tsaro Zagazola Makama ya ruwaito, mutum uku dauke da adduna da sanduna ne suka kutsa cikin kamfanin da nufin yin sata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun fara kai hari kan wasu jami’an tsaron farar hula na kamfanin Pilgrims Security, wadanda aka rahoto cewa sun sha da kyar daga harin.
Bayan haka, masu harin sun nufi katangar da ake amfani da ita wajen kula da zirga-zirgar jiragen sama, inda suka yi ƙoƙarin lalata ta don sace kayan da ke jikinta.
Jami’an tsaro da suka hada da rundunar NSCDC sun isa wurin cikin gaggawa tare da tarwatsa masu harin.
An kashe daya daga cikin 'yan daban
Bayan da aka kora su, wasu biyun daga cikin 'yan daban sun sake dawowa don cigaba da farmakin, lamarin da ya haifar da arangama da jami'an tsaro karo na biyu.
A lokacin gumurzu da jami’an tsaro, wani jami'in hukumar NSCDC ya samu nasarar harbe daya daga cikin masu harin a kafadarsa.
An garzaya da wanda aka harba zuwa asibitin gwamnati na Bajoga, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa bayan ya gudanar da gwaje-gwaje.
Masu harin sauran dai sun arce a na-kare, musamman bayan sanin cewa an harbi daya daga cikinsu, inda jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda suka fara bincike da farautarsu.

Source: Original
Kamfanin Ashaka na fuskantar hare-hare
Wannan lamari ya kara nuna matsalar tsaro da kamfanin simintin Ashaka ke fuskanta, wanda ke karkashin kamfanin Lafarge Africa a Funakaye, kilomita 120 daga Gombe.
A shekarar 2014, mayakan Boko Haram sun kai hare-hare a kamfanin sau biyu inda suka kwashe ababen fashewa da motocin kamfani, inji rahoton ICIR.
Sai dai, sabon harin na 2025 bai da alaka da ta’addanci, domin ana ganin barayi ne kawai suka kai farmaki domin satar kayan aiki.
A cafke 'yan Boko Haram a Gombe
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Gombe sun kama wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan ƙungiyar Boko Haram ne.
An ce 'yan sandan sun cafke mutanen ne a wani otal bayan samun sahihan bayanan sirri game da ayyukansu na ɓarna.
Lokacin samamen, an rahoto cewa jami’an 'yan sandan sun gano kuɗi, layu da kayan sawa a cikin wata jakar fata mai launin baƙi.
Asali: Legit.ng

