'Yan Bindiga Sun Sace Mutane Sama da 100 bayan kai Mummunan Hari Kebbi
- Aƙalla mutane 127 ne aka sace yayin da wasu suka rasa rayukansu a harin 'yan bindiga a ƙauyukan Danmuntari da Ali na ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a Kebbi
- Rahotanni sun ce maharan sun farmaki ƙauyukan ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe a ranar Litinin, 27 ga Mayu, 2025, inda suka yi ta harbe-harbe ba kakkautawa
- Jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji, ‘yan sanda da masu gadin gari sun shiga aikin ceto domin kubutar da mutanen da 'yan bindiga masu garkuwar suka sace
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi - Wasu gungun ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a ƙauyukan Danmuntari da Ali da ke kusa da iyakar jihar Kebbi da Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan sun hallaka mutane shida tare da sace wasu 127 yayin da suka kai harin.

Source: Facebook
Harin ya faru ne da safiyar Litinin, 27 ga watan Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 9:00 na safe, kamar yadda Zagazola Makama ya tabbatar a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan hari ya sake tayar da hankulan al’ummar yankin, musamman ganin yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da ƙaruwa duk da kokarin jami’an tsaro.
'Yan bindiga sun kashe mutane 6 a Kebbi
BBC ta wallafa cewa maharan sun isa garin Danmuntari da Ali a kan manyan babura tare da bindigogi, inda suka bude wuta kan fararen hula.
Mutane shida da suka haɗa da Malam Mudaha, Al’ameen Mohammed, Safwan Abubakar, Tanko Mohammed, Ibrahim Garba da Inno Mudaha (mace) ne suka rasa rayukansu a harin.
An kai gawawwakin zuwa asibitin Kebbi
Bayan harin, an kwashe gawawwakin waɗanda suka mutu zuwa babban asibitin Wasagu domin tantance su da gudanar da binciken likita kafin mika su ga iyalansu domin jana'iza.
Har yanzu dai babu cikakken bayani kan lafiyar mutanen da aka sace, sai dai jami’an tsaro na ci gaba da aikin ceto domin gano inda aka kaisu.

Kara karanta wannan
Bayan ƴan daba sun kashe DPO a Kano, an sake hallaka ɗan sanda da mutane 3 a Benue
Jami’an tsaro sun fara aikin ceto mutane a Kebbi
Wata majiya daga hukumar ‘yan sanda ta ce akwai jinkiri wajen kai agaji ga mazauna yankin sakamakon tsananin dazuka da tsaunuka da ke hana sauƙin samun dama.
Sai dai yanzu haka an tura haɗaɗɗun jami’an tsaro daga rundunar sojoji, ‘yan sandan kwantar da tarzoma da kuma jami’an sa-kai domin ceto mutanen da aka sace.

Source: Facebook
An ɗora laifin kan ‘yan bindiga daga Zamfara
Rahotanni sun ce maharan sun fito ne daga jihohin makwabta, musamman Zamfara, inda ake zargin suna da mafaka a dazukan yankin.
Masu tsaro sun bayyana cewa harin na cikin jerin hare-haren da ake kaiwa don hana mutane zaman lafiya da ci gaba a yankin, kuma suna cigaba da aiki don cafke masu laifi.
An kama 'yan kasar waje a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama wasu 'yan kasar Pakistan da ake zargi da safarar makamai.
Kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ne ya bayyana haka ga manema labarai a Borno.
Manjo Janar Abubakar ya bayyana cewa 'yan kasashen waje suna taimakon 'yan ta'adda da bayanai da horo a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
