Jami'an DSS da Sojoji Sun Yi Rubdugu kan 'Yan Bindiga, an Kashe Miyagu da Dama

Jami'an DSS da Sojoji Sun Yi Rubdugu kan 'Yan Bindiga, an Kashe Miyagu da Dama

  • Jami'an tsaro na hukumar DSS da sojoji sun yi aiki tare wajen ragargazar ƴan bindiga a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya
  • A yayin aikin haɗin gwiwar da suka yi, sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga da dama waɗanda ake zargin mayaƙa ne na tantiran ƴan ta'adda, Dogi Gide da Leyi
  • Bayan ragargazar ƴan bindigan, jami'an tsaron sun kuma buƙaci a turo jiragen yaƙi don ƙarisa ragowar ƴan bindigan da suka tsere zuwa cikin daji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Wani aikin haɗin gwiwa tsakanin jami’an hukumar tsaro ta DSS da sojojin Najeriya suka gudanar a jihar Neja, ya yi sanadiyyar kashe ƴan bindiga da dama.

Jami'an tsaron sun hallaka ƴan bindiga masu yawa waɗanda ake zargin mayaƙa ne na tantiran ƴan ta'adda, Dogo Gide da Leyi.

Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga a Neja
Jami'an tsaro sun hallaka 'yan bindiga a Neja Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Neja

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa har cikin fada, sun yi awon gaba da basarake a Nasarawa

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa aikin ya fara ne ranar Talata, lokacin da ƴan ta’adda suka kai hari garin Chibani da ke cikin ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja, cewar rahoton jaridar The Nation.

Rahotanni sun ce ƴan bindigan sun kashe wani mai suna Ayuba Isah sannan suka bar wani ɗan sanda da wani Alhaji Shuaibu ɗauke da raunin harbin bindiga.

A ranar Laraba kuma, ƴan bindigan da suka kai 200 ɗauke da mugayen makamai, sun kai hari sansanin tsaro da ke garin Kuchi, a cikin ƙaramar hukumar Munya.

Jami'an DSS da sojoji sun ragargaji ƴan bindiga

Majiyar ta ce musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ƴan bindigan ya kai ga kashe da dama daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere ɗauke da raunuka iri-iri.

Majiyar tsaron ta bayyana cewa ƙarin jami'ai da aka turo daga Galadima Kogo zuwa Kuchi ya taimaka matuƙa wajen raunana ƙarfin ƴan bindigan, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Wata majiya daga ɓangaren tsaro ta kuma bayyana cewa an hangi tarin shanun da ake kyautata zaton an sace su, suna ƙetare kogin Kusasu a yankin Galadima Kogo na ƙaramar hukumar Shiroro.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki kauyuka a Neja, an tafka gagarumar barna

Jami'an DSS
Jami'an DSS da sojoji sun fatattaki 'yan.bindiga a Neja Hoto: @OfficialDSSNG
Source: Twitter

Majiyar ta ce an karkata shanun ne zuwa wani wuri da ake zargin maɓoyar ƴan bindiga ce a yankin Borisudna/Kwaki, a cikin ƙaramar hukumar Shiroro.

Jami’an DSS da sojojin Najeriya da ke yankin sun tuntuɓi rundunar sojin sama ta Najeriya domin turo jiragen yaƙi, tare da fatan cewa za su iya fatattakar ragowar ƴan bindigan da suka tsere.

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kutsa har cikin fada sun yi awon gaba da basarake a jihar Nasarawa.

Ƴan bindigan sun kai harin ne inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi a cikin dare a ƙaramar hukumar Kokona ta jihar.

Rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta bayyana cewa ta fara ƙoƙarin ganin ta kuɓutar da basaraken cikin ƙoshin lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng