'Mutum sama da 10,000 aka Yiwa Kisan Gilla a Mulkin Tinubu," Amnesty Int'l
- Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty Int'l ta caccaki yadda gwamnatin Bola Tinubu ke riko da tsaro a cikin shekaru biyu
- Shugaban kungiyar na Najeriya, Mista Isa Sanusi ya bayyana cewa gwamnatin ta gaza cika alkawarin da ta dauka na kare rayuka
- Ya ce sama da mutum 10,000 aka kashe a karkashin mulkin Tinubu na shekaru biyu kawai, yayin da lamarin ke kara kacamewa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya, Amnesty Int'l, ta bayyana cewa rashin tsaro ya yi kamari daga lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki zuwa yau.
Kungiyar ta ce a cikin shekara biyu da suka gabata, fiye da mutane 10,217 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da kungiyoyin 'yan bindiga ke kai wa a jihohin Arewacin Najeriya.

Source: Twitter
The Guardian ta wallafa cewa rahoton da kungiyar ta fitar ya nuna cewa jihar Binuwai ce ta fi samun matsala, inda aka kashe mutane 6,896, sai kuma jihar Filato da aka kashe akalla 2,630.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amnesty Int'l ta bayyana cewa rikicin ya kara muni duk da alkawarin da gwamnatin Tinubu ta dauka na inganta tsaro a Najeriya.
Amnesty Int'l ta soki gwamnati kan tsaro
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban Amnesty Int'l a Najeriya, Isa Sanusi, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da gaza cika alkawarin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Ya bayyana cewa:
“Yau shekaru biyu kenan da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki da alkawarin inganta tsaro. Amma maimakon hakan, lamarin ya kara tabarbarewa, domin gwamnati ta kasa kare hakkin 'yan Najeriya.”
Isa Sanusi ya ce dole ne Shugaba Tinubu ya dauki mataki cikin gaggawa wajen fuskantar kalubalen tsaro da ke sake kunno kai a fadin kasar.
Ya ce sake fitowar Boko Haram da sauran kungiyoyin yan ta'adda ya nuna matakan tsaron da ake dauka yanzu ba su da inganci.
Amnesty Int'l: 'Ta'addanci na karuwa a Najeriya'
Shugaban ya kara da cewa wasu sababbin kungiyoyin 'yan bindiga sun bayyana a wannan lokaci, ciki har da Lakurawa a jihohin Sakkwato da Kebbi da kuma Mamuda a jihar Kwara.
Ya ce an kai hare haren da ya jawo asarar daruruwan rayuka a jihohin Binuwai, Borno, Katsina, Sakkwato, Filato da Zamfara.
A jihar Zamfara kadai, kauyuka 638 ne 'yan bindiga suka lalata gaba daya, yayin da kauyuka 725 ke karkashin ikon 'yan bindiga a kananan hukumomi 13 na jihar.
Ya ce:
“Tashe-tashen hankula a Zamfara na ci gaba da daukar hankali, inda ake kai hare-hare kusan kullum. A cikin shekaru biyu da suka gabata, fiye da mutane 273 aka kashe yayin da aka sace 467, musamman a karamar hukumar Maru."
Sojoji sun kalubalanci Amnesty Int'l
A baya, kun samu labarin cewa Rundunar sojin Najeriya da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta duniya, Amnesty Int'l, sun yi musayar yawu kan kisan fararen hula a Najeriya.
Shugaban kungiyar, Isa Sanusi ya zargi sojojin Najeriya da kai hare-haren sama da suka yi sanadiyyar mutuwar fararen hula akalla 436 a cikin shekaru takwas da suka gabata.
Amma daraktan labarai na rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana cewa sun gayyaci Amnesty Int'l don tattaunawa kan zarge-zargen da suka yi, amma ki zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


