2027: Sanatoci Sun Gano Dalilin Kara Karfin Boko Haram da Sauran 'Yan Ta'adda

2027: Sanatoci Sun Gano Dalilin Kara Karfin Boko Haram da Sauran 'Yan Ta'adda

  • Sanatoci sun bayyana cewa karuwar hare-haren Boko Haram da 'yan bindiga na da nasaba da shirin zaben 2027 da ake fuskanta a Najeriya
  • Sun bukaci gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike mai zurfi kan yiwuwar hannun wasu mutane da ke shirin tayar da rikici don dalilai na siyasa
  • Majalisar Dattawa ta bukaci karin matakan tsaro da tallafi ga mutanen da lamarin ya shafa a yankunan Arewa da ake fama da miyagu da 'yan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A zaman da Majalisar Dattawa ta yi ranar Laraba, Sanatoci sun nuna damuwa kan yadda hare-haren 'yan ta'adda ke kara yawaita a sassa daban-daban na kasar nan.

Sanata Shuaibu Isa Lau daga Taraba ne ya dauko batun a matsayin matsalar da ke bukatar kulawar gaggawa.

Kara karanta wannan

Atiku ya tono manyan 'kurakuran' Tinubu a shekara 2, ya yi raddi mai zafi

MAjalisa
Sanatoci sun alakanta matsalar tsaro da zaben 2027. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Sanata Lau ya samu goyon baya daga sanatocin jam’iyyar APC, Sunday Karimi da Danjuma Goje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatocin sun bayyana cewa irin wannan lamari ya faru kafin zaben 2015, kuma akwai yiwuwar wasu ‘yan siyasa ke shiryawa tayar da rikici idan suka fuskanci faduwar zabe a 2027.

Maganar Sanata Karimi kan matsalar tsaro

Sanata Karimi ya bayyana cewa a cikin makonni biyu da suka gabata, 'yan bindiga sun sace akalla mutane 30 a mazabarsa.

Ya tunatar da cewa gwamnan jihar Borno ya zargi wasu jami’an tsaro da hannu a hada baki da Boko Haram, wanda ke nuna akwai wani nufi na siyasa a ta'adin.

Sanata Goje ya nemi bincike kan matsalar tsaro

Sanata Danjuma Goje ya ce wannan ba karon farko ba ne, yana mai cewa tashin hankali yana faruwa a wurare da dama da suka hada da Bauchi da Taraba.

Ya jaddada cewa akwai bukatar a duba yiwuwar cewa wadannan hare-hare suna da alaka da shirin zaben 2027, yana mai cewa kada a dauki lamarin da wasa.

Kara karanta wannan

Bayanin da Bola Tinubu ya yi wa Najeriya bayan cika shekara 2 a kan mulki

Sanata Goje
Sanata Goje ya bukaci a yi bincike kan matsalar tsaro. Hoto: Muhammad Adamu Yayari
Source: Facebook

Majalisa ta bukaci karin matakan tsaro

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya nuna bakin ciki kan yadda ake kashe jama’a a kullum, inda ya bayyana cewa bai kamata mutane 70 su mutu a lokaci guda ba.

Ya bukaci hukumomin tsaro su kara kaimi, su tura jami’ai da kuma samar da tsarin sintiri na zamani don dakile hare-haren gaba.

Matsalar tsaro: Majalisa ta yi shiru na minti 1

Majalisar ta bukaci hukumomin NEMA da NEDC su gaggauta kai dauki ga mutanen da suka tsinci kansu cikin bala’i a jihohin Taraba, Bauchi da Plateau.

Sanatocin sun kuma yi shiru na minti daya domin girmama wadanda suka rasa rayukansu a rikicin da ya faru a yankunan.

'Ana taimakon 'yan ta'adda daga ketare,' Sojoji

A wani rahoton, kun ji cewa kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ya ce akwai hannun 'yan kasashen waje a matsalar tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kaddamar da manyan ayyuka a Kano da Legas kafin sallar layya

Janar Abdulsam Abubakar ya bayyana cewa wasu 'yan kasashen waje na taimakawa 'yan Boko Haram da ISWAP.

Kwamandan sojin ya bayyana haka ne bayan kama wasu 'yan kasar Pakistan da ake zargi suna da alaka da safarar makamai zuwa Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng