Mahajjaciya Ƴar Najeriya Ta Yi Abin Yabo da Ta Tsinci Sama da Naira Miliyan 8 a Makkah
- Wata ƴar Najeriya daga cikin mahajjatan bana, Hajiya Zainab ta mayar da Dala 5,000 da ta tsinta ga mai su dan ƙasar Rasha a Saudiyya
- Hajiya Zainab ta tsinci kuɗin, da suka kai kimanin ₦8,240,000 a masallacin Harami da ke Makkah, amma ba ta yi wata-wata ba ta maida wa mai su
- Hukumar kula da alhazai ta ƙasa (NAHCON) da hukumar jin daɗin alhazan jihar Filato sun tabbatar da faruwar wannan lamarin a Saudi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Wata mahajjaciya 'yar Najeriya mai suna Hajiya Zainab daga Jihar Filato ta mayar da dala $5,000 da ta tsinta ga mai su dan kasar Rasha a Saudiyya.
Kuɗin da suka kai kimanin ₦8,240,000 bisa farashin musaya na ₦1,648 kan kowace dala, Hajiya Zainab ta tsince su ne a Masallacin Harami da ke birnin Makkah a ranar Talata.

Kara karanta wannan
Bayan yanke mata hukunci, kotu ta umarci a ba jarumar TikTok, Murja Kunya muƙami a CBN

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa Hukumar Kula da Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da Hukumar Alhazai ta jihar Filato ƙarƙashin jagorancin Daiyabu Dauda sun tabbatar da faruwar lamarin.
Hajiya Zainab ta fara shan yabo a Saudiyya
Wannan kyakkyawar ɗabi'a da halin kirki da mahajjaciyar ta nuna a ƙasa mai tsarki ya ja hankali, inda ake ci gaba da yaba mata bisa abin da ta yi.
Da yake bayyana halin kirki da amana na Hajiya Zainab, Ɗaiyabu Dauda ya ce:
"Ta nuna hali mai kyau na gaskiya da amana ta hanyar mayar da dala $5,000 da ta tsinta a Masallacin Harami ga mai kuɗin. Wannan halin kirki ne da ya cancanci yabo."
NAHCON ta fara tattaunawa da Saudiyya
A wani bangare kuma, hukumar NAHCON ta bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa da hukumomin Saudiyya domin buɗe tsarin bayar da biza ga maniyyatan da ke son zuwa Hajji.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Fatima Sanda Usara, Mataimakiyar Darakta mai kula da harkokin yada labarai da hulɗa da jama'a ta fitar a ranar Laraba.
Ta bayyana cewa ƙasashe da dama ciki har da Najeriya sun matsa lamba ga gwamnatin Saudiyya ta cire takunkumin dakatar da bayar da bizar aikin hajji.

Source: Twitter
Da yiwuwar Saudiyya ta dawo da bada bizar Hajji
Fatima Usara ta ce hukumar na fatan samun sakamako mai kyau daga tattaunawar da ake ci gaba da yi da hukumomin Saudiyya, rahoton Vanguard.
“Muna da kwarin gwiwar cewa za a samu sakamako mai kyau, kuma da zarar hakan ya tabbata, NAHCON za ta kwashi alhazai da aka riga aka yi wa rajista zuwa ƙasa mai tsarki,” in ji ta.
Ta kuma bayyana cewa hukumar ta bar wasu ma’aikatanta cikin shiri domin fuskantar kowanne irin yanayi idan aka buɗe tsarin samar da biza.
Mahajjaciyar Najeriya ta rasu a Saudiyya
A wani labarin, kun ji cewa wata mahajjaciya daga Jihar Edo, Hajiya Adizatu Dazumi ta rasu yayin gudanar da aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya.
Rahotanni sun nuna cewa matar tana da shekaru 75 a duniya, kuma asalinta ta fito ne daga garin Jattu Uzairue da ke karamar hukumar Etsako ta Yamma.
Matar ta kamu da rashin lafiya ne bayan kammala dawafi a Ka’aba, sannan aka garzaya da ita zuwa asibitin King Fahad, inda Allah Ya ƙarɓi rayuwarta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

