Hakeem Baba Ya Sake Sukar Gwamnati, Ya Fadi Masifar da Tinubu Zai Jefa Talaka

Hakeem Baba Ya Sake Sukar Gwamnati, Ya Fadi Masifar da Tinubu Zai Jefa Talaka

  • Tsohon hadimin Bola Tinubu, Hakeem Baba Ahmed ya caccaki sabon bashin da gwamnatin tarayya ke shirin karbowa a waje
  • Ya bayyana takaicinsa, inda ya ce ba karbo bashin ne matsala ba, rashin amfani da shi ta hanyar da ya dace ne tashin hankalin
  • Hakeem Baba Ahmed ya shawarci majalisun kasar nan a kan su duba halin matsin tattalin arziki kafin amincewa da bukatar Tinubu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaTsohon mashawarcin Kashim Shettima a kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana damuwarsa kan sabon bashin da gwamnatin tarayya ke shirin ciwo wa.

A ranar Talata ne ya nemi sahalewar majalisar wakilai domin karbo sabon bashi, kuma takardar da shugaban zauren, Abbas Tajuddeen ya karanta ta fadi iya kudin da za a karbo.

Kara karanta wannan

Bayan rufe ofishin PDP, Wike ya fadi babbar matsalar da yake fuskanta a Abuja

Hakeem
Hakeem Baba Ahmed ya fusata kan shirin gwamnatin Tinubu na karbo sabon bashi Hoto: Bayo Onanuga/Hakeem Baba Ahmed
Source: Facebook

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa cewa Abbas Tajudeen ya ce kudin da Tinubu ke son ya karbo ya hada da $21.5b (N34tr) da Yuro biliyan 2.2 (N3.96trn) da Yen na Japan biliyan 15 (N164.7bn) da kuma Yuro miliyan 65 (N116.79bn) a matsayin tallafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakeem Baba ya fusata da gwamnatin Tinubu

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Baba-Ahmed ya bayyana fargabarsa game da illar da wannan sabon bashin zai iya haifar wa tattalin arzikin Najeriya.

Ya bayyana cewa akwai rashin dacewa a karbo sabon bashin ganin yadda tattalin arzikin Najeriya a yanzu ke cikin mawuyacin hali.

Ya ce:

“Anya, wanan sabon bashi da gwamnatin tarayya take so ta ciwo mana, har tiriliyon dari da sittin da biyu (N162 trn), alheri ne gare mu kuwa?”

Hakeem Baba Ahmed ya kara da cewa:

“A halin da muke ciki, inda tattalin arzikin mu yake dukushe, kuma daman muna dauke da bashi mai ban tsoro, wannan bashin da a ke so a karbo yana da tada hankali,” ya kara da cewa.

Kara karanta wannan

Tsaro: Dan majalisa ya yiwa ministan Buhari fata-fata kan sukar gwamnatin Tinubu

Shawarar Hakeem Baba Ahmed ga majalisa

Hakeem Baba Ahmed ya bayyana cewa kamata ya yi wakilan al'umma a majalisar wakilai da ta dattawa su tsaya tsayin daka wajen nazarin kudirin bashin, kafin su amince da shi.

Ya ce:

“Idan da masu wakiltanmu a majalisan wakilai da dattawa masu jin kukan mu ne, da sai mu ce su yi wa wannan kudirin da zai kara mana nauyi a kan nauyi, kyakykyawan duba tukuna."

A cewarsa, basussuka sun riga sun yiwa Najeriya nauyi, wanda hakan ke kara dagula tsarin tattalin arziki da rayuwar talakawa.

Hakeem Baba na takaicin karo bashi

Ya kara da nuna damuwa, inda ya ce ci gaba da ciwo bashi ba tare da tsayayyen tsarin amfani da shi ba na iya cutar da ‘yan Najeriya da kuma ‘ya’yansu a gaba.

A kalamansa:

“Yanzu da mu da 'ya'yan mu zamu zauna shake da bashi da talauci ke nan?” ya tambaya.

Tsohon hadimi a ofishin shugaban kasa ya bukaci a sake duba batun bashin, tare da jaddada cewa idan za a karbi bashi, to sai dai a tabbatar da cewa za a yi amfani da shi bisa amana.

Kara karanta wannan

NEC: Atiku, Wike da wasu jiga jigan PDP sun yi watsi da babban taron jam'iyya

Hakeem: 'Tinubu ya hakura da takara'

A baya, kun ji cewa stohon mashawarcin musamman a fadar shugaban ƙasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya hakura da neman takara a 2027.

Ya bayyana cewa hakura da takarar zai ba Shugaba Tinubu damar gina tarihi mai kyau da kuma sauya tsarin siyasar Najeriya zuwa hanya mai tsafta da cike da haɗin kai da cigaba.

Baba-Ahmed ya shawarci shugaban ƙasa da ya mayar da hankali wajen gyara tsarin siyasa da inganta rayuwar ‘yan kasa maimakon mai da hankali wajen tsayawa takara a karo na biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng