Shekara 2 a Mulki: Buhari Ya Aika Sako ga Shugaba Bola Tinubu
- Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aika da saƙo ga mai girma Bola Tinubu yayin da ya cika shekara biyu a kan kujerar mulki
- Muhammadu Buhari ya nuna cewa sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta kawo sai an kai zuciya nesa dangane da su
- Tsohon shugaban ƙasan ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da marawa Tinubu baya a ƙoƙarin da yake yi na saita fasalin ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu murna bisa cikar shekara biyu da ya yi yana mulkin Najeriya.
Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yayin da jam’iyya da gwamnati ke murnar wannan lokaci, ya kamata a tunatar da ƙasa cewa shugabanci abu ne wanda yake buƙatar ci gaba.

Source: Facebook
Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya sanya a shafinsa na X a ranar Laraba, 28 ga watan Mayun 2025.
Muhammadu Buhari ya buƙaci a goyawa APC baya
Buhari ya yi kira da a ci gaba da bai wa gwamnatin APC goyon baya yayin da take cika shekara ta biyu a ofis.
Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana cewa sauye-sauyen da ake ƙoƙarin aiwatarwa ba za su yi nasara dare ɗaya ba, sai a sannu a hankali.
Ya yi gargaɗin cewa dole ne a kare waɗannan sauye-sauye da gyare-gyare daga faɗawa cikin sukar da take da salo irin na siyasa.
Tsohon shugaban ya bayyana goyon bayansa ga ƙoƙarin da gwamnatin ke yi wajen rage talauci da hauhawar farashi, matsaloli da suka fi shafar talakawa.
Ya bayyana cewa duk da girman wannan aiki, bai kamata a bar gwamnati ita kaɗai ta yi shi ba.
“Dole ne ɓangaren masu zaman kansu da mu a matsayin ƴan ƙasa mu haɗa hannu ta hanyoyi daban-daban da muke iya yi.”
- Muhammadu Buhari
Buhari ya ba ƴan Najeriya shawara

Kara karanta wannan
"An talauta 'yan Najeriya": Tsohon ministan Buhari ya yi raga raga da gwamnatin Tinubu
Ya kuma shawarci ƴan Najeriya da su ci gaba da kasancewa cikin fatan alheri da ƙwarin gwiwa kan makomar ƙasar nan.
Buhari ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su riƙa bin gwamnati sannu a hankali ta yadda ba za a ɗora mata abin da ya fi ƙarfinta ba.
Buhari ta taya Bola Tinubu murna
“Kada mu ɗora wa gwamnati nauyin da ya fi karfinta."
“Ina taya Shugaba Tinubu murna da zuciya ɗaya bisa cika shekara biyu a mulki. Allah Ya ba ka hikima da kulawa wajen ci gaba da jagoranci."
- Muhammadu Buhari
Saraki ya zargi Buhari da gallaza masa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da gallaza masa.
Saraki ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasan ya hana shi sakat ne saboda ya nuna rashin gamsuwa kan yadda yake karɓo basussuka ba tare da tsari ba.
Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya ce majalisar dattawan da ya shugabanta ta fuskanci matsin lamba daga wajen Muhammadu Buhari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
