Tashin Hankali: Gini Mai Hawa 2 Ya Ruguje kan Mutane, An Rasa Rayukan Mutum 3

Tashin Hankali: Gini Mai Hawa 2 Ya Ruguje kan Mutane, An Rasa Rayukan Mutum 3

  • Gini mai hawa biyu da ake kan ginawa ya rushe a Ikorodu, Legas, inda mutane uku suka mutu, yayin da aka ceto wasu tara da ransu
  • LASEMA ta ce ta tura kungiyoyin agajinta na na Lion, Tiger da Eagle daga sansanoninta na Agbowa, Alausa da Cappa zuwa wurin
  • Hukumar ta ce har yanzu ba a gano musabbabin lamarin ba amma ana ci gaba da bincike, kuma an rushe ragowar ginin don kare mutane

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Gini mai hawa biyu da ake ginawa ya rushe a kusa da wani gidan mai da keyankin Ikorodu a jihar Lega inda mutane uku suka mutu yayin da wasu suka jikkata.

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) ce ta fitar da wannan sanarwa a ranar Laraba, inda ta ce ta kai agajin gaggawa bayan samun kira daga yankin.

Kara karanta wannan

Yadda aka samu 'dan sandan da aka kashe a Kano da hannu a kisan 'barayin kaji' tun 2021

LASEMA ta tabbatar da rugujewar wani gida mai hawa 2, inda mutane 3 suka mutu
Wani ginin bene mai hawa biyu da ya rufta kan mutane a jihar Legas. Hoto: @followlasema1
Source: Twitter

Mutane 3 sun mutu da gini ya rufta a Legas

LASEMA ta ce ta tura kungiyoyi daga ofisoshinta na Agbowa, Alausa da Cappa zuwa wurin da abin ya faru domin gudanar da ceto, inji rahoton Channels TV.

A cewar rahoton, bayan isowar kungiyoyin agajin na LASEMA, irinsu Lion, Tiger da Eagle zuwa inda abin ya faru, an tarar da mutane uku a cikin baraguzan ginin da ya rushe.

Sai dai duk wani kokari na ceto su ya ci tura, inda aka tabbatar da mutuwar mutanen uku, wadanda suka hada da yarinya ‘yar shekara 16 da kuma maza biyu.

Amma kuma hukumar ta ce an ceto wasu maza tara da ransu, kuma jami’an sashen kula da lafiyar gaggawa na LASEMA sun ba su kulawa nan take.

LASEMA ta kai agaji bayan ruftawar gini

A halin yanzu ba a san musabbabin rushewar ginin ba, kasancewar ana kan gudanar da aikin ginin ne a lokacin da ya rushe. Hukumar ta ce tana kan yin bincike don gano dalilin faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Awanni da rufe hedikwatar PDP, kotu ta sanya a kamo mata darakta a hukumar FCTA

Domin gudanar da aikin ceto, hukumar ta aika da manyan motocin hakar kasa, ciki har da motar kwasar kasa don tone baraguzai da budewa jami'ai hanyar aikin ceto.

An girka fitilun haska wajen domin ci gaba da aikin cikin dare yayin da aka mika gawarwakin wadanda suka mutu ga rundunar ‘yan sanda na Igbogbo domin ci gaba da bincike.

LASEMA da sauran hukumomin tsaro sun kai agaji da gini mai hawa 2 ya rufta kan mutane a Legas
Jami'an hukumar LASEMA na kokarin ceto mutane yayin da wani ginin bene ya rufta kan mutane a Legas. Hoto: @followlasema1
Source: Facebook

Hukumomin tsaro sun kai daukin gaggawa

The Nation ta rahoto cewa ana ci gaba da aikin ceto a wurin, inda LASEMA ta ce an fara rushe sauran bangaren ginin da bai rushe ba domin kare lafiyar jami’an agaji.

Aikin agajin ya samu hadin gwiwar hukumomi da dama ciki har da ma’aikatar kashe gobara da ceto ta jihar Legas da kuma hukumar tsaron cikin gida ta Legas (LNSC).

Sauran hukumomin da suka shiga aikin sun hada da NSCDC, ‘yan sanda, hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas, da kuma hukumar kiyaye hadurra ta ƙasa (FRSC).

Dalilin rushewar gine-gine a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, masana sun ce rashin shugabanci nagari a fannin injiniyanci na daga cikin manyan dalilan da ke haddasa yawaitar rushewar gine-gine.

Kara karanta wannan

Kano: Fusatattun matasa sun cinnawa ofishin ƴan sanda wuta, an ji abin da ya faru

Kididdiga daga rahotanni daban-daban ta nuna cewa daga 1974 zuwa 2025, akalla mutane 1,595 ne suka rasa rayukansu sakamakon irin wadannan hadurra, mafi yawansu a jihar Legas.

Farfesa Okorie Uche ya bukaci a mayar da hankali kan ba da dammar jagoranci ga kwararrun injiniyoyi, tare da fifita aminci da inganci a kan riba ta gajeren lokaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com