Kwastam Ta Cafke Mota Makare da Sinadaran Hada Bam da wasu Haramtattun Kaya
- Hukumar Kwastam ta kama wata mota da ke dauke da sinadaran da ake zargin ana hada bama-bamai da su a Najeriya
- Jami’an kwastam sun kama mutum daya da ake zargin yana da alaƙa da motar da kayan haɗa bam, bayan sun yi ido biyu da motar
- Baya ga kayan hada bam, kayayyakin da aka kama sun hada da kudin kasashen waje da suka kai darajar Naira miliyan tara
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen Seme ta sanar da kama wata mota da ake zargin tana ɗauke da kayan hada bam.
Jami'an hukumar sun yi nasarar damke motar ne wani samame da suka kai yayin gudanar da sintiri da bincike kan kayayyakin da ake shigo da su cikin ƙasar.

Source: Facebook
An bayyana hakan ne a wani bidiyo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, inda aka nuna yadda jami’anta ke gudanar da bincike a kan motar da aka kama a hanyar Legas zuwa Badagry.
Ana shirin shigo da kayan hada bam Najeriya
BBC Hausa ta wallafa cewa, an gano cewa cikin motar akwai kwalaye guda shida da ke ɗauke da sinadarin mercury – wani muhimmin abu da ake zargin ana amfani da shi wajen hada bam.
Shugaban hukumar Kwastam na reshen Seme, Kwanturola Ben Oramalugu, ya bayyana cewa an cafke mutum guda da ake zargin yana da alaƙa da motar.
Ya jaddada cewa wannan nasara tana nuna irin himma da ƙoƙarin da hukumar Kwastam ke yi wajen tabbatar da tsaro da kare ƙasar daga barazanar ta’addanci.

Source: Twitter
Oramalugu ya ƙara da cewa wannan aiki na cikin tsarin matakan hana fasa-kwauri da sauran ayyukan da suka sabawa doka a iyakokin kasar nan.
Sauran kayayyakin da kwastam ta kama
Baya ga motar da ake zargin tana ɗauke da kayan haɗa bam, hukumar ta kuma cafke wasu kayayyaki da dama da suka sabawa dokar ƙasar.
Kayayyakin sun haɗa da kuɗin ƙasashen waje daga ƙasashe irin su Birtaniya, Kanada da Amurka, da darajarsu ta kai kimanin N9m wanda ya ci karo da dokokin harajin kayayyaki.
Sauran abubuwan da aka kama sun haɗa da robar ganyen wiwi guda 553, buhunan shinkafa daga waje guda 1,415, jarkokin man fetur 750 da kuma magunguna da ba su da rajista.
Oramalugu ya ce za a mika kayayyakin ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace, ciki har da gurfanar da waɗanda ake zargi.
Hukumar Kwastam ta yi kame a Kano
A wani labari, kun ji cewa hukumar kwastam ta ce jami’anta sun kama kuɗin ƙasashen waje da suka haɗa da Dalar Amurka 1.1 miliyan da kuma Riyal na Saudiyya 135,900 a Kano.
A cewar sanarwar da kakakin hukumar, Abdullahi Maiwada, ya fitar an gano kudin a cikin jakunkunan dabino yayin da ake binciken kayayyakin wani fasinja filin jirgin sama.
Rahotanni sun ce an gurfanar da wanda ake zargin da kudin a kotu, kuma ta bayar da umarnin a kwace kudin tare da mika su ga gwamnatin tarayya, domin ci gaba da gudanar da bincike.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


