Sojoji Sun Gano 'Yan Kasashen Waje na ba Boko Haram Horo, An Kama Mutum 4

Sojoji Sun Gano 'Yan Kasashen Waje na ba Boko Haram Horo, An Kama Mutum 4

  • Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa wasu ‘yan ƙasashen waje na baiwa ‘yan Boko Haram da ISWAP horo a kan amfani da fasahohin yaki
  • Laftanar Janar Abdulsalam Abubakar ya ce an kama wasu ‘yan Pakistan hudu da ake zargi da safarar makamai ga ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas
  • Sojoji sun bukaci ƙarin haɗin gwiwa da ƙasashe makwabta da kuma aikin leƙen asiri domin dakile 'yan ƙetare da ke baiwa ‘yan ta’adda horo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Rundunar sojin Najeriya ta bayyana damuwa kan yadda wasu 'yan ƙasashen waje ke baiwa kungiyoyin Boko Haram da ISWAP horo a kan dabarun yaki,

Rundunar sojin ta ce cikin taimakon da ake ba 'yan ta'addan akwai ba su horo wajen amfani da jirage marasa matuka da kuma ƙera abubuwan fashewa.

Kara karanta wannan

ADC: Maganar hadakar adawa ta yi nisa, ana dab da cimma matsaya kan zaben jam'iyya

Major General Abdulsalam Abubakar
Sojoji sun kama 'yan Pakistan 4 bisa zargin safarar Makamai. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Leadership ta wallafa cewa kwamandan Operation Hadin Kai, Laftanar Janar Abdulsalam Abubakar, ne ya bayyana haka ga manema labarai a birnin Maiduguri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, kama wasu ‘yan ƙasar Pakistan hudu da ake zargi da safarar makamai ga ‘yan ta’adda na nuna yadda haɗin kai tsakanin masu tayar da kayar baya da ƙasashen waje ke ƙaruwa.

Ana horar da 'yan ta'adda daga kasar waje

Laftanar Janar Abubakar ya bayyana cewa bata gari daga ƙetare na baiwa ‘yan ta’adda horo kan dabarun amfani da kayan zamani wajen kai hare-hare da leƙen asiri.

Ya ce hakan ya sa Boko Haram da ISWAP suka fara amfani da jirage marasa matuka wajen kai farmaki da kuma sanin duk wani motsin dakarun soji.

A cewarsa:

“Hakan na nuna yadda ‘yan ta’adda ke ƙara wayewa wajen amfani da dabaru irin na zamani, kuma hakan barazana ce ga ƙasar nan.”

Safarar makamai: An kama ‘yan kasar Pakistan 4

Kara karanta wannan

Sojoji sun farmaki 'dan ta'adda Kachalla Murtala, sun ruguza sansaninsa a Katsina

Kwamandan ya ce sojoji sun kama ‘yan ƙasar Pakistan hudu da ake zargi da sayar da makamai ga kungiyoyin ta’addanci, wanda bincike ya nuna suna da alaka da ‘yan Boko Haram da ISWAP.

Ya ce wannan ya ƙara tabbatar da cewa akwai haɗin gwiwa tsakanin wasu ƙasashen waje da ‘yan ta’addan da ke yaki da Najeriya.

Janar Abubakar ya ce ya dace a fuskanci lamarin da cikakkiyar haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da ƙasashe makwabta domin katse hanyar samun tallafin kayan aiki.

Sojoji
Sojoji sun bukaci hadin kai wajen yaki da ta'addanci. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

'Yan ta'adda na yaki ne da Najeriya,' Sojoji

A cewar sojojin, yakin ba wai tsakanin ‘yan ta’adda da rundunar soji ba ne, yaki ne da Najeriya gaba ɗaya, domin kuwa ba sojoji kadai ake kai wa hari ba, har da al’ummar ƙasa.

Ya bukaci ‘yan jarida su rika daukar yaki da ta’addanci da muhimmanci wajen wayar da kan jama’a, tare da bayyana irin sadaukarwar da sojoji ke yi a cikin mawuyacin hali na zafi da sanyi.

Yadda ake zargin masu daukar nauin Boko Haram

A cikin shekaru da dama da suka gabata, ana ta bayyana damuwa kan yadda wasu ƙasashen ƙetare ke da hannu wajen ƙarfafa ayyukan Boko Haram da ISWAP a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ribadu ya fadi dabarar da suka yi wajen kashe 'yan ta'adda 13,500 a shekara 2

Rahotanni da dama sun nuna cewa ba kawai cikin gida wannan fitina ta samo asali ba, akwai wasu ƙasashen waje da ke ɗaukar nauyin horo, makamai da kuma dabarun fasaha ga ‘yan ta’addan da ke addabar yankin Arewa maso Gabas.

A cewar jami’an tsaro, ana horar da ‘yan ta’adda a kasashen waje kan amfani da fasahohin zamani kamar jiragen leƙen asiri marasa matuki da kuma ƙera abubuwan fashewa da na hari.

Wannan na nuni da cewa akwai wata ƙullalliyar siyasa ko tattalin arziki da ke baiwa ‘yan ta’addan damar samun ƙarin ƙarfi.

Kama ‘yan ƙasar Pakistan da ake zargin da safarar makamai wani babban misali ne na yadda ƙasashe na ƙetare ke shigo wa da hannu cikin wannan rikici.

Wannan na ƙara jaddada cewa yakin da Najeriya ke yi da ta’addanci ba zai yi nasara ba sai da hadin kai da ingantaccen leƙen asiri tsakanin Najeriya da ƙasashe makwabta.

'Yan ta'adda sun kai hari Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari wata unguwa a birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun kai hari ne cikin dare inda suka sace mutane kafin jami'an tsaro su fatattake su.

Mutanen yankin sun bukaci a samar da ofishin 'yan sanda a kusa da su domin a rika kawo musu dauki idan aka kawo musu hari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng