Kisan Sarkin Adara: Kotu Ta Samu El Rufa'i da Laifi, an Ci Tarar Shi N900m
- Kotun tarayya a Kaduna ta yanke hukunci cewa tsohon gwamna Nasir El-Rufai, da wasu jami'an gwamnati sun kan take hakkin dan Adam
- Kotun ta umurci El-Rufai da sauran mutanen da su biya sama da N900m a matsayin diyya ga dattawan da aka tsare ba bisa ka'ida ba a 2019
- Lauyan masu karar ta ce wannan hukunci nasara ne ga al'umma da ishara kan rashin dacewar cin zarafi da amfani da iko ba bisa doka ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ta yanke hukunc kan karar da aka shigar da Nasir El-Rufa'i da wasu mutane.
Kotun ta umarci tsohon gwamnan jihar Kaduna da wasu jami'an ‘yan sanda su biya sama da N900m ga wasu dattawan Adara da aka tsare su ba bisa doka ba a shekarar 2019.

Source: Twitter
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa an tsare mutanen ne a bayan kisan da aka yi wa Sarkin Adara na wancan lokacin.
Hukuncin da Mai Shari’a Hauwa’u Buhari ta yanke a ranar Talata, 27 ga Mayu, 2025, ya bayyana cewa an take hakkin dan Adam wajen tsare dattawan.
An bayyana cewa wannan hukunci ya fito ne daga karar da Mr. Awemi Maisamari da wasu dattawan Kudancin Kaduna suka shigar bayan tsare su na tsawon watanni.
Sarkin Adara: El-Rufa'i ya kama mutane
An kama Awemi Maisamari wanda ya kasance shugaban kungiyar ci gaban Adara, tare da wasu dattawa takwas.
Cikin wadanda aka kama har da tsohon kwamishina Bawa Magaji da kuma tsohon kwamishinan ‘yan sanda.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an kama su ne bayan kisan sarkin Adara, Dr Raphael Galadima a 2019.
El-Rufai da ke matsayin gwamna a lokacin ya zargi Maisamari da cewa yana daga cikin matsalolin tsaro a yankin Kajuru.
An bayyana cewa lamarin ne ya sa aka tsare dattawan na tsawon watanni kafin daga baya a sake su.
Kotu ta ci tarar Nasir El-Rufa'i N900m
Mai Shari’a Hauwa’u Buhari ta bayyana cewa El-Rufai ya dauki matakin kama dattawan ba tare da wani hujja ba, wanda hakan ya sabawa doka.
Kotun ta umurce shi da ya biya diyyar N900m a matsayinsa na wanda ya ba da umarnin kama su kai tsaye.
Baya ga haka, kotun ta kuma umurci rundunar ‘yan sanda da Sufeto Janar da kuma Kwamishinan ‘yan sanda na Kaduna su biya N10m a matsayin diyya.

Source: Getty Images
Lauya ga masu karar, Gloria Ballason ta bayyana hukuncin a matsayin nasara mai muhimmanci kan take hakkin dan Adam da kuma amfani da iko ba bisa ka’ida ba.
Nasir El-Rufa'i ya hadu da Rabiu Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa Nasir El-Rufa'i ya hadu da madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Abuja.
An hango tsohon gwamnan jihar Kadunan tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suna magana a wani masallacin Juma'a.
Ganawar tsofaffin gwamnonin ta dauki hankalin jama'a musamman lura da yadda 'yan adawa ke shirin hadaka domin tunkarar APC a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

