Najeriya Ta Kwato Dalolin da aka Sace, An Dawo da $763.7m, £6.4m ga Gwamnati

Najeriya Ta Kwato Dalolin da aka Sace, An Dawo da $763.7m, £6.4m ga Gwamnati

  • Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya ce an dawo da kuɗin sata sama da Dala $763m da Fam £6.4m daga kasashen waje zuwa Najeriya tsakanin 2017 zuwa 2024
  • Ya bayyana cewa an zuba kuɗin da aka dawo da su a cikin ayyukan raya ƙasa kamar titin Lagos-Ibadan da kuma shirin tallafin kuɗi ga talakawa
  • Babban lauyan ya kara da cewa an sa ido sosai kan yadda aka kashe kuɗin da aka dawo da su, inda aka yi aikin da sa idon ƙungiyoyi masu zaman kansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya bayyana cewa an dawo da wasu daga cikin kuɗin Najeriya da aka sace.

Ya bayyana cewa kuɗin da aka samu nasarar dawo da su asusun gwamnati sun kai $763,734,000 da £6,472,610 da aka sace daga Najeriya tsakanin shekarar 2017 zuwa 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kinkimo bashin dala biliyan 21.1 domin wasu ayyuka a Najeriya

Tinubu
Gwamnatin tarayya ta samu nasarar kwato kudin da aka sace daga asusun kasar Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Fagbemi ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin buɗe taro kan dawo da dukiyoyi da ma’aikatarsa ta shirya mai taken: “Haɗin gwiwa domin dawo da dukiyoyi da sarrafa su yadda ya kamata.”

Yadda aka kwato kuɗin Najeriya

Leadership News ta wallafa cewa Fagbemi ya ce daga cikin adadin da aka dawo da shi, miliyan $102.88 da £2,062,000 ne aka samu daga shekarar 2024 zuwa yanzu.

Babban lauyan ya kara da bayyana yadda ma’aikatarsa ke aiki da takwarorinta da hukumomi daga ƙasashen waje kamar Amurka, Birtaniya, da yankin Bailiwick of Jersey.

Tinubu
Gwamnati ta ce an yi amfani da kudin da aka kwato wajen taimakon talaka Hoto; Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Haka zalika, ana aiki da ƙasashen Ireland da Switzerland domin aiwatar da yarjejeniyoyi da dawo da dukiyoyin da aka sace.

Fagbemi ya ce:

"Daga 2017 zuwa 2024, an zuba Dala $659,900,000 da Fam £6,472,610 da aka dawo cikin shirin tallafin kuɗi na Conditional Cash Transfer ga 'yan kasa, da kuma wasu muhimman ayyukan raya ƙasa."

Kara karanta wannan

Masu ibada sun faɗa tarko, ƴan bindiga sun sace mutum 3 bayan sun dawo daga wa'azi

An sa ido kan dawo da kudin Najeriya

Fagbemi ya ce an sa ido kan shirin bayar da tallafin kuɗi ta wata ƙungiyar haɗin gwiwar ƙarƙashin ANEEJ, inda ake wallafa rahotannin akan shafinsu na yanar gizo.

Ya ƙara da cewa:

"A ɓangare guda, ƙungiyar CLEEN Foundation ce ta sa ido kan yadda aka kashe kuɗin da aka dawo da su a ayyukan PIDF, tana fitar da rahotannin lokaci-lokaci a shafinta: www.assetmonitoring.org.ng.
"Shafukan yanar gizo na ƙungiyoyin da na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya su ne dandamalin da Najeriya ta amince da su kan yarjejeniyoyin dawo da dukiyoyi da kuma yadda ake sarrafa su."

Yaki da talauci: Najeriya za ta kashe Daloli

A wani labarin, mun wallafa cewa a wani gagarumin mataki na bunkasa harkar noma a Najeriya, gwamnatin tarayya ta kaddamar da sabon shiri na Value Chain Nigeria (VCN).

Gwamnatin ta ce za a gudanar da shirin ne tsawon shekaru takwas, inda za a yi aiki kai tsaye a jihohin Arewa tara, kuma an tanadi kudin da ya kai Dala miliyan 158.15 domin tabbatar da shi.

Ƙasashen da za su amfana da wannan gagarumin shiri sun hada da: Borno, Bauchi Kano, Katsina, Kebbi. Jigawa, Sakkwato, Yobe da Zamfara domin inganta harkar noma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng