'Mata Masu Sanya Sarkar Kafa Karuwai ne': Fasto Ya ba da Sabuwar Fatawa

'Mata Masu Sanya Sarkar Kafa Karuwai ne': Fasto Ya ba da Sabuwar Fatawa

  • Shugaban cocin Salvation Ministries, Fasto David Ibiyeomie, ya soki matan da ke yin shigar banza, ya ce karuwai ne ke sanya sarka a kafa
  • Faston ya gargadi matan da ke bayyana nononuwa da 'yan kamfansu, yana mai cewa hakan rashin kunya ne da rashin da'a ga Kirista
  • Kalaman Fasto Ibiyeomie sun tayar da kura, inda wasu ke ganin yana yawan yin maganganun da ke tayar da jijiyoyin wuya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Lagos – Shugaban cocin Salvation Ministries, Fasto David Ibiyeomie, ya nuna damuwarsa kan yadda 'yan mata ke yin shigar banza da yin adon da bai dace ba da sunan wayewa.

Yayin da yake wa’azin a cocinsa da ke Port Harcourt, Fasto Ibiyeomie ya bayyana cewa mata sun daina sanya sarka a kafa don ado, sai dai don wata mummunan manufa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan daba sun farmaki kamfanin simintin a Gombe, an kashe mutum 1

Fasto David Ibiyeomie ya ce mata masu sanya sarkar kafa karuwai ne
Shugaban cocin Salvation Ministries, David Ibiyeomie | Hoton kafa sanye da sarka. Hoto: @DavidIbiyeomie/X, Sani Hamza/Staff
Source: Twitter

"Sanya sarkar kafa alamar karuwanci ce" - Fasto

Jaridar Punch ta rahoto malamin addinin yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wasu daga cikinku kuna son bin zamani, amma ba ku san mummunar illa da hakan yake da shi ga rayuwarku da ta al'umma ba."

Faston ya kara da cewa:

“Idan mace ta sanya sarka a kafarta, to tana fadawa mutane cewa, ‘Ni karuwa ce.’
“Asalin ma’anar sanya sarka a kafa ita ce: ‘Karuwanci, ba wai irin wanda ake yi a cikin otal ba, a'a, irin wanda ke nufin cewa, zan ba ka dama idan ka nema."

Fasto Ibiyeomie ya jaddada cewa sanya irin wannan sarkar a kafa ba wai wani ado ne fasaha ba, illa kawai tallata kai a matsayin 'karuwa'.

Fasto ya gargadi mata kan fito da nonuwa waje

Ya ja kunnen 'yan mata da su guji irin wannan shiga da ke nuna rashin tarbiya da kuma kara yaduwar halayen banza a cikin al’umma.

Kara karanta wannan

2027: Atiku da manyan 'yan siyasa 7 da suka dauki aniyar raba Tinubu da ofis

Faston ya kuma soki matan da ke nuna surar jikinsu, yana mai cewa hakan rashin kunya ne da ya saba da ɗabi’ar Kirista.

A cewar malamin addinin:

“Kin fito kin bayyana wa dukkanin mutanen duniya nononki, kuma kina cewa mutane suna damunki da maganganu na rashin da'a?”

Ibiyeomie ya kuma soki yadda mata ke sanya tufafi masu huda ko na roba da ke bayyana jikin mace da kayanta na ciki, yana mai cewa hakan lalacewar ɗabi’a ce.

Fasto David Ibiyeomie ya caccaki matan da ke fitar da tsiraici da sanya sarkar kafa
Shugaban cocin Salvation Ministries, David Ibiyeomie | Hoton kafa sanye da sarka. Hoto: @DavidIbiyeomie/X, Sani Hamza/Staff
Source: Twitter

Kalaman malamin addinin sun jawo ce-ce-ku-ce

Maganganunsa sun jawo ce-ce-ku-ce a dandalin sada zumunta, inda wasu ke goyon bayansa, wasu kuma na ganin ya yi tsauri da ya wa.

Sai dai malamin bai ja baya a kan wannan fatawa ta shi ba, inda ya ƙare da cewa "yadda kika nunawa mutane kanki, shi ne yadda za su dauke ki."

A watan Afrilu kuma, Faston ya yi ikirarin cewa Yesu Almasihu bai taba yin hulɗa da matalauta ba a rayuwarsa, yana mai cewa masu imani su guji zama da talakawa.

'Wasu don ado suke sanya sarkar kafa' - Amina

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Sanata ya halarci zaman majalisar dattawa sanye da rigar Tinubu

A zantawar mu da wata mai shagon kwalliya da gyaran jiki, Amina Lawal a jiha Kaduna, ta ce malamin addinin ya zafafa kalamansa, domin mata da yawa suna sanya sarkar kafa don kwalliya.

Amina Lawal ta shaida wa Legit Hausa cewa:

"Gaskiya akwai gyara a maganarsa, ba duka aka taru aka zama daya ba. Don matan banza na yin ado, ba shi ke nufin cewa duk wacce ke irin adon mutuniyar banza ba ce.
"Mata da yawa na sanya sarkar kafa domin ado. Ko ni ina sanya wa a cikin gida na, saboda mijina yana so. Ba na sanya wa lokacin da ina budurwa, amma da yake yana so, na koyi sanya wa, to don ka ganni da ita sai ka ce ni mutuniyar banza ce?"

Amina Lawal ta nemi malamin da ya rika sassauta kalamansa, musamman ganin cewa maganarsa na iya jawo bacin rai daga mabiyansa da sauran wadanda ba addini daya suke ba.

An caccaki Fasto Ibiyeomie a kan hudubarsa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar CAN da fitaccen Fasto Abel Damina sun caccaki Fasto David Ibiyeomie na Salvation Ministries kan wa’azin da ya yi inda ya soki talauci.

Kara karanta wannan

An hallaka DPO a Kano yayin da rikici ya barke tsakanin matasa da 'yan sanda

CAN da Fasto Damina sun mayar da martani ne bayan Ibiyeomie ya bayyana cewa Annabi Isa (AS) yana kin talakawa kuma Allah ba ya son talauci.

A wani bidiyo da Ossai Ovie Success ya wallafa a kafafen sada zumunta, Ibiyeomie ya ce: "Yesu bai taɓa shiga gidan talaka ba," yana nuni da cewa talauci ba shi da matsayi a wurin Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com