Matashi ya kure jaruma Rahama Sadau, ta daddana masa ashar kan sarkar kafarta

Matashi ya kure jaruma Rahama Sadau, ta daddana masa ashar kan sarkar kafarta

  • Jaruma Rahama Sadau ta dannawa wani ashar a Twitter bayan ya zagi mahaifiyarta kan batun sanya sarkar kafa da take yi
  • Tun farko dai wani matashi ne ya wallafa hoton ta inda yake tambayar ma'anar sarkar kafarta, ta sanar masa cewa ta zinari ce mai tsada
  • Sai dai babu jimawa wani ya zo yana zagin mahaifiyarta kan dalilin da zai sa ta saka sarkar, bata bata lokaci ba ta dannawa mahaifinsa ashar

Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumunta ta Twitter ya wallafa hoton jaruma Rahama Sadau sanye da sarkar kafa inda ya bukaci karin bayani kan dalilin da yasa take sanyawa.

Babu bata lokaci kuwa aka dinga bashi amsa game da fahimtar jama'a kan matan dake saka sarka kafar. Wasu sun ce 'yan madigo ke sanyawa yayin da wasu suka ce kwalliya ce kawai ta mata wacce addini bai haramta ba.

Kara karanta wannan

"Aljanna Zai Muku Wahalar Shiga": Mutane Sunyi Martani Kan Wani Wasa Da MC Tagwaye Da Danuwansa Suka Yi Wa Jinjirarsa

Jaruma Rahama Sadau
Matashi ya kure jaruma Rahama Sadau, ta daddana masa ashar kan sarkar kafarta. Hoto daga @Rahma_Sadau
Asali: Twitter

Wani kuwa da yace yayi bincikensa a google, yace ma'ana biyu gareta. Idan mace ta sanyata a kafar dama toh tana bayyana ita budurwa ce kuma tana neman miji, idan kuwa a hagu ne, toh mata aure ce. Sai yace a dama Rahama Sadau ta saka tata, ga me sha'awa sai ya taya.

Ganin wannan, jaruma Rahama Sadau ma ta tanka inda ta bada amsa da cewa: "Ya kai anonymous, wannan sarkar gwal ce mai matukar tsada, da fatan na amsa maka tambayarka."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai da babu jimawa wani daga cikin masu tsokacin ya mayar mata da amsa cewa, "Don uwarki aka ce ki saka a kafa?"
Babu bata lokaci jarumar taje ta mayar masa da martani kamar haka: "Eh Fa, Uban babanka ne yace in saka a kafa."

Babu jimawa aka fara cece-kuce kan lamarin, inda da yawa daga cikin jama'a ke goyon bayan jarumar da ta rama zagin uwarta da aka yi. Wasu kuwa cewa suka yi duk da bai kyauta ba, bai dace ta biye masa har tayi masa martanin zagi ba. Hakan yana nufin sun zama daya kenan.

Kara karanta wannan

Shigar musulmai na burgeni, zan iya muslunta, inji 'yar fim Mercy Aigbe da ta auri Musulmi

Rahama Sadau ta sadaukar da dukkan kudin da fim dinta na Nadiya zai kawo ga gidauniyar mabukata

A wani labari na daban, Rahama Sadau, ta sadaukar da dukkan cinikin fim din ta na Nadeeya ga gidauniyar taimakawa mabukata da gajiyayyu.

Labarin da Legit.ng ta tattaro daga shafin Labaran Kannywood a Twitter shi ne: A wata tattaunawa ta kai tsaye da gidan talabijin da rediyo na Liberty ya yi da jaruma Rahama Sadau, ta sanar da cewa duk cinikin da ta yi a fim din ta da ake haskawa a sinima yanzu haka ta sadaukar da shi ga gidauniyarta ta tallafawa mabukata mai suna Ray of Hope.

Asali: Legit.ng

Online view pixel