Masu Ibada Sun Fada Tarko, Ƴan Bindiga Sun Sace Mutum 3 bayan Sun Dawo daga Wa'azi
- Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu ɗaliban coci uku a hanyarsu ta dawowa daga wurin karatun Littafi Mai Tsarki a jihar Ondo
- Majiyoyi daga cocin sun bayyana cewa maharan sun kira waya, sun nemi a haɗa masu Naira miliyan biyar a matsayin kuɗin fansa
- Rundunar ƴan sanda reshen jihar Ondo ta ce dakarunta sun fara farautar maharan da nufin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace ɗaliban coci a jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya.
Rahoto ya nuna cewa wasu ƴan cocin Deeper Christian Life Ministry sun shiga hannun masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo.

Source: Original
Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun sace masu ibadar ne a ranar Litinin, a yayin da suke dawowa daga taron karatun Littafi Mai Tsarki a yankin Kasemola, kusa da Ogbese.
Yadda aka sace masu ibada a Ondo
A wani saƙo da cocin ta fitar a Whatsapp, ta buƙaci ƴan uwa da abokan arziki su sanya waɗanda aka sace a addu'a domin Allah Ya kuɓutar da su.
Saƙon cocin ya ce:
"Ina kwana 'yan’uwa masu albarka. Don Allah a taya mu da addu'a. An sace wasu daga cikinmu guda uku jiya bayan karatun Littafi Mai Tsarki watau Bayibul a Kasemola, yankin Ogbese. Muna neman Ubangiji ya kubutar da su.
Ƴan sanda sun fara farautar maharan
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Ondo, Olusola Ayanlade, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar salula.
Ya ce 'yan sanda sun fara bin sawun masu garkuwan domin kubutar da waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya.

Kara karanta wannan
"Tinubu ya dage sai an magance matsalar tsaro a 2025," Badaru ya faɗi halin da ake ciki
Sai dai, Ayanlade ya ce har yanzu ba zai iya tabbatar da adadin wadanda aka sace ba, yana mai cewa:
"Zan iya tabbatar da cewa an samu rahoton sace mutane, amma ba zan iya tabbatar da yawan wadanda aka dauka ba a yanzu."

Source: Facebook
Shin ƴan bindigar sun nemi kuɗin fansa?
Wani ɗan cocin ya bayyana wa wakilin Channels tv cewa masu garkuwar sun kira waya, sun bukaci Naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa.
"Mun fara zaman addu'a a cocin, kuma ana ta tattaunawa tsakanin mambobi don tara kudin fansar. Mun aika da saƙon gargadi zuwa ga shugabannin mu na sauran yankuna domin daukar mataki," in ji shi.
Jihar Ondo na ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro, inda sace-sacen mutane domin neman kuɗin fansa ke ƙara yawaita.
Yan bindiga sun sake shiga Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa ƴan bindiga sun sake kai hari yankin ƙaramar hukumar Kubwa a babban birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun ce maharan sun shafe kusan awa guda suna cin karensu babu babbaka kafin isowar dakarun ‘yan sanda.
Wani mazaunin unguwar da lamarin ya faru, ya ce maharan sun yi nasarar sace wani namiji da mace, amma daga bisani macen ta gudo daga hannunsu.
Asali: Legit.ng
