Abu Ya Girma: 'Bam' Ya Tashi a kusa da Sojoji a Abuja, Mutane Sun Shiga Fargaba
- Wani abu da ake zaton bam ne ya tashi a tashar motocin da ke daura da barikin sojoji na Mogadishu a babban birnin tarayya Abuja
- Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa yau Litinin, ta ce tuni aka samu nasarar shawo kan lamarin
- Shaidu sun bayyana cewa mutane sun firgita a lokacin da bam ɗin ya tashi, kowa ya yi takansa domin tsira da rayuwarsa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - An shiga fargaba da wani abu da ake kyautata zaton bam ne ya tarwatse a wata tashar motoci a da ke babban birnin tarayya Abuja.
Bayanai sun nuna cewa lamarin ya auku ne a wata tashar mota da ke daura da barikin sojojin Najeriya da ke Mogadishu a Abuja yau Litinin, 26 ga watan Mayu, 2025.

Source: Twitter
Rundunar sojoji ta tabbatar da tashin bam
Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata gajeruwar sanrwa da ta wallafa a shafinta na X.
Rundunar sojin ta bayyana cewa an shawo kan lamarin gaba ɗaya, kuma babu wani dalili na shiga tashin hankali ko fargaba.
"Wani abu ya fashe a tashar motar da ke daura da barikin sojoji na Mogadishu a Abuja, an shawo kan lamarin a halin yanzu, za mu fitar da ƙarin bayani nan gaba," in ji sanarwar.
Yadda mutane suka firgita da lamarin
Shaidu sun bayyana cewa ana zargin wani ne ya yi yunkurin kai harin kunar bakin wake amma ya rasa ransa a lokacin da bam din ya fashe.
Jama'a dai sun firgice loƙacim da bam ɗin ya tashi, inda masu wuce, masi jiran mota da sauran waɗanda ke wurin suka fara gudun neman tsira.
Yan Sanda sun yi magana kan abin da ya faru
Rundunar Ƴan Sanda ta Najeriya ta fara bincike kan fashewar wacce aka ce ta girgiza gefen Abuja, a kan hanyar Mararaba-Nyanya, a ranar Litinin.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan FCT, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Ta ce rundunar ta samu rahoton gaggawa ranar 26 ga Mayu, 2025, da misalin karfe 2:50 na rana, dangane da fashewar da ta auku a gefen hanyar.

Source: Twitter
Kakakin ƴan sandar ta ce:
"Bayan samun rahoton, jami’an sashen kwance bam (EOD) sun garzaya wurin da lamarin ya faru.
"Nan da nan suka kewaye wurin domin yin bincike da tabbatar da cewa babu wata barazana ga masu wucewa da mazauna yankin.”
Adeh ta ƙara da cewa an samu wani mutum ɗaya da ya ji rauni kuma tuni aka garzaya da shi asibiti domin a duba lafiyarsa.
Bam ya tashi da ƙananan yara a Borno
A wani labarin, kun ji cewa ƙananan yara sun tono bam ba tare da sank ba a ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno.
Rahotanni sun nuna. cewa kananan yara biyar ne suka jikkata, ɗaya daga cikinau ya rasa hannunsa sakamakon tashin bam.
Bayanai sun nuna an birne bam din ne a cikin ramuka kusa da wata gada da ke hanyar zuwa wurin aikin gina sabon masallacin Juma'a na Mafa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


