Mutanen Gari Sun Huce Fushinsu kan Fulani bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Malamin Addini

Mutanen Gari Sun Huce Fushinsu kan Fulani bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Malamin Addini

  • Ƴan bindiga sun kai hari a gidan wani malamin addinin Kirista a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Plateau
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka Rabaran Mimang Lekyl tare da raunata matarsa da ƴar uwarta a yayin harin
  • Kisan da aka yi wa malamin addinin, ya jawo wasu fusatattun mutane sun ƙona gidajen Fulani a yankin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Ƴan bindiga sun hallaka wani Rabaran mai suna Mimang Lekyil, da ke ƙauyen Kwakas a gundumar Mushere cikin ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.

Hakazalika ƴan bindigan sun raunata matar malamin addinin tare ƴar uwarta a yayin harin.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
'Yan bindiga sun kashe malamin addinin Kirista a Plateau Hoto: @CalebMutfwang
Source: Facebook

Wasu mazauna yankin sun tabbatarwa da jaridar Daily Trust aukuwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun hallaka Rabaran a Plateau

Sun bayyana cewa ƴan bindigan, waɗanda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun kai farmaki gidan faston ne da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Lahadi, a lokacin da iyalinsa ke shirin kwanciya barci.

Kara karanta wannan

Yadda rikicin kabilanci ya jawo asarar rayukan mutane a Taraba

Bishop Ayuba Matawal, wani mazaunin Bokkos wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa an sace matan biyu tun da farko, amma wasu ƴan sa-kai da matasan yankin sun ceto su.

“Eh, sun harbe Faston. Matan biyu da ke cikin gidan, matarsa da wata baƙuwa, an sace su, amma daga baya mazauna yankin suka taru suka bi ƴan bindigan suka ceto su."
"Ana zargin cewa sun zo ne don su sace Faston, ganin cewa sun tafi da matan."

- Bishop Ayuba Matawal

Ya ƙara da cewa an ajiye gawar Faston mai kimanin shekaru 70 da haihuwa a daƙin ajiye gawarwaki na Luna da ke Bokkos.

An ƙona gidajen Fulani

A halin da ake ciki kuma, wasu fusatattun mazauna yankin sun ƙona gidaje da dama mallakin Fulani a ƙauyen Dingak, wani sansanin makiyaya da ke gundumar Mushere.

Saeed Adamu, shugaban matasan Fulani a Bokkos, ya bayyana cewa an ƙona gidajen mambobinsu da dama sakamakon kisan Faston.

'Yan bindiga sun yi barna a Plateau
An kona gidajen Fulani a jihar Plateau Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yayin da ya yi Allah-wadai da kisan Faston, Sa'eed Adamu ya buƙaci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin tare da gurfanar da su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro a Katsina, an samu asarar rayuka

Shugaban matasan ya kuma yi Allah-wadai da ƙona gidajen Fulani, yana mai cewa babu wata sahihiyar shaidar da ke nuna cewa makiyaya ne suka kashe malamin addinin.

"Mun ji labarin kisan Faston, amma babu wani bincike da ya nuna cewa mambobinmu ne suka yi kisan."
"Haka ake yawan yi a irin waɗannan lokuta. Muna kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin."

- Sa'eed Adamu

Ƴan bindiga sun hallaka jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun hallaka jami'an tsaro na rundunar C-Watch a jihar Katsina.

Ƴan bindigan sun kashe jami'an tsaron ne bayan sun kai musu wani harin kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Matazu.

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru, ya kai ziyarar gani da ido inda ƴan bindigan suka farmaki jami'an tsaron.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng