Kano: Fusatattun Matasa Sun Cinnawa Ofishin Ƴan Sanda Wuta, An Ji Abin da Ya Faru

Kano: Fusatattun Matasa Sun Cinnawa Ofishin Ƴan Sanda Wuta, An Ji Abin da Ya Faru

  • Fusatattun matasa sun kona ofishin ‘yan sanda bayan rikici ya barke a Kano, kan rasuwar Abdullahi Musa a hannun ‘yan sanda
  • Masu zanga-zangar na zargin cewa DPO na Rano, Baba Ali, ya yi wa Musa dukan kawo wuka yayin tambayoyi, lamarin ya zama ajalinsa
  • Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da lamarin, ta ce za ta gudanar da bincike yayin da aka ce an raunata DPO da wasu mutane biyu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - An samu barkewar tashin hankali a karamar hukumar Rano da ke jihar Kano ranar Litinin, bayan mutuwar wani matashi mai suna Abdullahi Musa.

An ce Abdullahi ya mutu a hannun 'yan sanda, lamarin ya fusatar da al'ummar Rano, inda suka fara zanga-zanga har ta kai ga kona ofishin ‘yan sanda na garin.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke a tsakanin matasa da yan sanda a Kano, ana fargabar an kashe DPO

Zanga-zanga da ta barke a Kano ta jawo an cinnawa ofishin 'yan sanda wuta
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, yayin wani taron 'yan sandan jihar. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Mutuwar matashi a ofishin 'yan sandan Kano

Rahoton Leadership ya nuna cewa cewa an kama Abdullahi Musa bisa zargin karya dokar zirga-zirga, amma ya rasu yayin da ake masa tambayoyi a ofishin 'yan sandan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidu sun zargi DPO na Rano da ake kira Baba Ali da azabtar da marigayin ta hanyar duka, lamarin da suka ce shi ne ya yi sanadin mutuwarsa.

Wani mazaunin Rano mai suna Muhammad ya bayyana cewa:

“DPO din Rano ya yi wa saurayin duka sosai. Daga baya muka ji cewa ya mutu a hannunsu. Wannan ne ya tayar da tarzoma."

Mutuwar Musa ta tayar da hankalin matasa, inda suka mamaye ofishin 'yan sanda suna neman adalci.

Shaidu sun ce rikicin ya kazanta ne bayan da 'yan sanda suka bude wuta kan masu zanga-zanga, inda matasa biyu suka jikkata.

Abin da ya jawo aka kona ofishin 'yan sanda

Wani daga cikin masu zanga-zangar da ya zanta da CITAD Radio, kuma ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

Kara karanta wannan

Makiyaya dauke da makamai sun harbe malamin addini a Makurdi, sun sace mutane 2

“Zanga-zanga ce ta lumana. Muna so ne kawai mu ji gaskiyar abin da ya faru da Abdullahi Musa. Sai kawai suka fara harbe-harbe.

Rahotanni sun ce matasan da suka jikkata, Hassan Salisu Hassan da Muhammad Ibrahim, na karbar magani a asibitin gwamnati na Rano.

Wani mazaunin Rano, Malam Yusuf Auwalu, ya shaidawa manema labarai cewa:

“Rana ce mai cike da bakin ciki a gare mu. Abdullahi Musa ba dan ta’adda ba ne. An kama shi ne kawai, sai ga shi ya mutu. Muna bukatar adalci.”

Muhammad ya kara da cewa:

“A cikin fushi, matasan suka fara jifar 'yan sanda da duwatsu, daga baya suka banka wa ofishin wuta.”
Rundunar 'yan sanda ta ce za ta dauki matakin da ya dace yayin da aka kona ofishinta a Kano
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Rundunar 'yan sanda za ta fara bincike

Rahotanni sun kuma bayyana cewa DPO Baba Ali ya samu munanan raunuka a lokacin rikicin, kuma yana karbar magani.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Legit Hausa ta iya tabbatarwa.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cewa za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta shirya yanke hukunci a kan matashin da ya babbake masallata 25

A shafinsa na Facebook, Kiyawa ya rubuta cewa: “Abin da yake faruwa a Garin Rano. Za a dauki matakin da ya kamata na bincike Insha Allah.”

Za a rataye wanda ya kona masallata a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotu ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same shi da laifin babbake masallata a jihar Kano.

Mai Shari’a Halhalatun Huza’i Zakariya ce ta yanke hukuncin, ta ce kotu ta gamsu da hujjojin da ke nuna Shafiu ya aikata kisan a watan Mayu, 2024.

Baya ga hukuncin kisa, an kuma yanke masa wasu karin hukunci guda biyu, wanda hakan ya kawo ƙarshen shari’ar da aka dade ana yi da matashin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com