'Yan Sanda Sun Ragargaji Masu Garkuwa da Mutane, an Kwato Makamai

'Yan Sanda Sun Ragargaji Masu Garkuwa da Mutane, an Kwato Makamai

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya ta samu nasarar hallaka wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne
  • Jami'an rundunar sun samu nasarar ne a wani samame da suka kai kan maɓoyar waɗanda ake zargin a Abuja
  • Hakazalika ƴan sanda sun kuma ceto wata dattijuwa da ƴan bindiga suka yi garkuwa da ita a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rundunar ƴan Sandan Najeriya ta bayyana cewa ta cafke mutane 12 da ake zargi da garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Hakazalika jam'ian rundunar sun ceto wata mata mai shekaru 80 da aka yi garkuwa da ita, sannan sun ƙwato bindigu da dama.

'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane
'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sanda na ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Litinin a shafin X.

Kara karanta wannan

Kishi kumallon mata: Yadda matar aure ta hallaka kishiyarta a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce jami'an rundunar ƴan sanda na Abuja da jihar Jigawa ne suka gudanar da ayyukan.

Ƴan sanda sun kashe miyagu

A cikin Abuja, jami’an ƴan sanda sun ragargaza wata ƙungiyar fashi da makami da kuma satar motoci da ke aiki a birnin.

Bisa bayanan sirri da aka samu, tawagar ƴan sanda ta tare miyagun a lokacin da suke shirin kai hari a Maitama.

Bayan an yi musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro, an hallaka ɗaya daga cikin sanannun ƴan ƙungiyar da ake nema ruwa a jallo, wato Abdulmuminu Bello, wanda aka fi sani da Babanle.

"Wani daga cikin sanannun masu laifi a ƙungiyar, Abdulmuminu Bello, wato Babanle, ya mutu a fafatawar, yayin da aka kama sauran mutum bakwai a wajen da lamarin ya faru."
"Waɗanda aka kama sun haɗa da Ibrahim Muhammad, mai shekara 22 wanda ya taba shiga gidan yari, Abubakar Abdullahi, mai shekara 22, Sarajo Yusuf, mai shekara 20, Sanusi Ali, mai shekara 51, Abubakar Sani, Isiaka Adamu da Abdullahi Isah."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro a Katsina, an samu asarar rayuka

"Kayan da aka ƙwato a wajen sun haɗa da bindigogi AK-47 guda huɗu, bindigogi guda biyu ƙirar gida tare da harsasai 10 masu nauyin 9mm, harsasai 11 masu nauyin 7.62mm, mota ƙirar Toyota Camry LE samfurin 2004, da kuma babur ƙirar Boxer mai launin ja."

- ACP Olumuyiwa Adejobi

Jami'an 'yan sanda
'Yan sanda sun ceto dattijuwar da aka sace a Kano Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

An ceto dattijuwar da aka sace

A wani samame na daban da aka kai a jihar Jigawa, ƴan sanda sun ceto wata dattijuwa ƴar shekara 80 mai suna Hajiya Hajara, wadda aka sace daga ƙauyen Sarbi, a ƙaramar hukumar Minjibir ta jihar Kano.

Bayanan sirri sun nuna cewa wasu ƴan bindiga kusan 12 ne suka sace matar, sannan suka yi ƙoƙarin shiga da ita ta jihar Jigawa.

"Ƴan sanda tare da hadin gwiwar ƴan sa-kai sun farmaki maboyar ƴan ta’addan da ke tsakanin ƙauyukan Danzomo da Medi."
"An yi musayar wuta da su, inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar biyar daga cikinsu, yayin da aka kama wasu biyar ciki har da shugabansu wanda ake kira Yahaya, mai shekara 35."

- ACP Olumuyiwa Adejobi

Ɗan sanda ya hallaƙa ɗalibi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ɗan sanda ya hallaka ɗalibin da ke kan hanyar zuwa zana jarabawar WAEC bisa kuskure a jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram a Borno

Lamarin mai ban tausayi dai ya faru ne lokacin da ɗalibin ke tafiya tare da mahaifinsa a kan babur.

Ɗan sandan dai ya yi harbin ne lokacin da suke bin wasu da ake zargin ƴan damfara ne a cikin birnin Ibadan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng