Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwar Duba Watan Sallar Layya a Najeriya

Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwar Duba Watan Sallar Layya a Najeriya

  • Kwamitin harkokin addini na fadar Sarkin Musulmi ya bayyana cewa Talata 27 ga Mayu, 2025, ita ce 29 ga Zul-Qa’ada 1446H, ranar fara duba watan Dhul Hijjah
  • An bukaci Musulmi su mika bayanan ganin watan ga hakimai ko dagatai don isar da su ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III
  • Muhammad Sa’ad Abubakar III ya dauki matakin ne domin tantance ranar da za a yi hawan Arafa da ranar babbar Sallah da za a yi Idi da yanka dabbobi a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa a ranar Litinin, 26 ga Mayu 2025, yana kira ga Musulmi da su fita duba jinjirin watan Dhul Hijjah a daren Talata, 27 ga Mayu.

Kara karanta wannan

Sallar layya: kasar Saudiyya ta fitar da sanarwar duba jinjirin wata

Ranar Talata, 27 ga Mayu dai ta yi daidai da 29 ga watan Zul-Qa’ada 1446, wata na biyun karshe a kalandar Musulunci.

Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi ya bukaci a fara duba watan sallah. Hoto: National Moon Sighting Committee
Source: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan maganar da Sarkin Musulmi ya yi ne a cikin wani sako da ofishin yada labaran masarautar Sokoto ya fitar a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Kwamitin Harkokin Addini na Majalisar Masarautar Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya bukaci Musulmi da su ba da hadin kai wajen gudanar da aikin.

Sanarwar ta bayyana cewa duk wanda ya ga jinjirin watan ya sanar da hakimi ko dagaci mafi kusa domin isar da labarin ga Sarkin Musulmi.

Ana jiran ganin wata don sallar layya

Neman jinjirin watan Dhul Hijjah na da matukar muhimmanci a Musulunci, kasancewar a watan ne ake gudanar da ibadun Hajji da kuma bikin babbar Sallah.

Musulmi a Najeriya da ma duniya baki daya na jiran tabbatar da ganin jinjirin watan domin sanin ranar da za a fara ayyukan Hajji da kuma ranar Sallah.

Sarkin Musulmi
An bukaci 'yan Najeriya su fita duba wata a gobe Talata. Hoto: National Moon Sighting Committee
Source: Facebook

Idan aka ga jinjirin watan a daren Talata, hakan na nufin Laraba 28 ga Mayu za ta kasance ranar farko ta Dhul Hijjah, kuma babbar Sallah za ta kasance ranar Juma’a 6 ga Yuni, 2025.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi magana yayin da aka hana shi shiga Saudiyya aikin Hajji

Sai dai in ba a ga jinjirin watan ba, to za a cika Zul-Qa’ada zuwa 30, kuma ranar farko ta Dhul Hijjah za ta koma Alhamis, yayin da Sallah za ta kasance Asabar 7 ga Yuni.

Kira ga yin addu'a da fita duba wata

Sanarwar ta kammala da addu’ar neman taimakon Allah wajen sauke wannan nauyi da aka daura wa al’umma.

An bukaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin addu’a domin zaman lafiya, hadin, tare da fatan yin sallah cikin cikakken tsaro.

Babbar sallah a Muslunci

A Najeriya, Musulmi na gudanar da bikin Babbar Sallah wato Eid el-Kabir da cikakken nishadi, ibada, da hadin kai.

Wannan biki na daya daga cikin manyan lokutan da ke hade al’umma, musamman a cikin gidaje, masallatai da kasuwanni.

Tun daga safiyar Sallah, Musulmi na shirya kansu da sabbin kaya, suna taruwa a masallatan Idi don gudanar da sallar raka’a biyu.

Bayan kammala sallar, limamai sukan yi huduba mai karfafa imani da tunatar da Musulmai mahimmancin sadaukarwa, kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya yi.

Daga nan ne ake ci gaba da yanka dabbobi – tunkiya, saniya, ko rago – wanda hakan na da ma’anar bin sunnah da girmama sadaukarwar Annabi Ibrahim.

Kara karanta wannan

Bidiyon Sanusi II da mataimakin gwamna yayin addu'ar cika shekara 1 a sarautar Kano

Ana raba naman ga iyali, makwabta da mabukata, domin tabbatar da cewa kowa ya samu daga cikin wannan ni’ima.

A garuruwa da kauyuka, ana gudanar da hawan sallah tare da rawar gargajiya, ziyarce-ziyarce da ciye-ciye. Yara kan more sabbin kaya da wasanni, yayin da manya ke karbar baki da hada kai wajen gudanar da bukukuwa.

Babbar Sallah lokaci ne na hadin kai da girmama juna, kuma Musulmi a Najeriya na daukar ta da muhimmanci fiye da komai.

Za a fara duba watan sallah a Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta fitar da sanawar kan duba watan babbar sallah a shekarar 2025.

Kotun kolin Saudiyya ce ta fitar da sanarwar, inda ta bukaci dukkan 'yan kasar da su fita duba watan.

Baya ga haka, hukumomin kasar Saudiyya sun bukaci duk wanda ya ga watan ya sanar da kotu mafi kusa da shi domin tabbatarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng